An Cafke Basaraken Gargajiya, Matarsa Da Dansa Bisa Zargin Garkuwa Da Mutane

0
243

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba.

RUNDUNAR tsaro ta hadin gwiwa a kuros riba wato operation Akpakwu ta cafke barasaraken kauyen Ikot Atambi dake karamar hukumar Akpabuyo jihar kuros riba Mai Suna Etiyin Atambi Eyo shi da matarsa da Dan su bisa zargin su da laifin kama mutane ana yin garkuwa dasu domin amsar kudin fansa.

Bayanan da wakilin mu ya ruwaito daka karkarar sun nuna cewa basarake Atambi Eyo yana da wani tsafaffen wuri da yake girka wadanda yake amfani da su wajen su kama masa duk wanda suka yi hari da Kuma masu aikata fashi da makami.

Dubun Basaraken ta cika ne a ranar Talata bayan da aka kyankyasawa jami’an tsaro, Kuma suka kai samame inda suka kama su.

Karamar hukumar Akpabuyo tayi kaurin  Suna wajen maboyar masu kama mutane ana yin garkuwa dasu.

Alfred Mboto Babban Mai  ba gwamnan Jihar kuros riba shawara kan harkokin tsaro, ya tabbatarwa wakilin mu na kudanci cewa Hakika wanda ake zargi Basaraken ya amsa laifinsa, yace shi da matarsa da Dan su nada Hannu a wajen kama mutane ana garkuwa dasu”.

Hakazalika, mataimakina musamman kan harkokin tsaron ya ce “an rusa gidansa na  unguwar masu galihu dake satellite town dake Kalaba Babban birnin jihar kuros riba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here