Za A Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ A Kaduna

0
171

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna, a ranar Litinin, ta kafa wata kwamiti da zai samar da tsari na karatu domin bawa malaman makarantar allo shaidar koyarwa a jihar.

Dakta Shehu Muhammad, kwamishinan Ilimi na jihar, wanda ya kaddamar da kwamitin a Kaduna ya ce karkashin sabon tsarin, malaman makarantun allo za su rika samun takardan shaidar malanta ta NCE.

Muhammad ya ce wannan matakin na cikin shirin da ake yi ne na yi wa karatun na tsangaya garambawul domin gwamutsa shi cikin tsarin ilimi tamkar na boko.

Ya bayyana karatun na almajiranci a matsayin tsari inda yaran musulmi masu kananan shekaru ke koyan ilimomi na addinin musulunci da tarbiya.

Kwamishinan ya ce duk da cewa musulmi har yanzu suna sha’awar tsarin, wasu sun bijiro da matsaloli cikinsa don haka akwai bukatar yi wa tsarin garambawul don ya dace da zamani.

“An dora wa kwamitin alhakin fidda tsari da zai samar da malaman makarantun allo da za su samu NCE kuma a iya daukansu aiki a makarantun frimare da sakandare.

“Kwamitin zai kuma samar da tsari ba bada horaswa ga malaman makarantun allo a jihar.

“Ana kuma sa ran kwamitin ya samar da tsarin yadda za a shigar da malaman makarantun allo zuwa tsarin koyarwa na zamani.

“Idan an kammala, za a mika tsarin ga hukumar ilimin kwalleji na kasa domin dubba yiwuwar amfani da shi a matakin kasa,” in ji shi.

Muhammad ya ce duk da cewa mafi yawancin malaman allo sun samu horasawa, sun haddace Al-Kurani, suna kuma da ilimin addinin musulunci, ba su da shaidar karatun da za a iya daukarsu aiki.

Ya ce an bawa kwamitin makonni shida don kammala aikinta.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here