An Kama ‘Yan IPOB Da Suka Kashe ‘Yan Sanda a Jihar Akwa Ibom

0
191

Daga Musa Muhammad Kutama.

HEDKWATAR Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce an kama wasu daga cikin mambobin kungiyar Indigenous Peoples of Biafra (IPOB) ‘da ke da hannu wurin kisa da kona yan sanda a Akwa Ibom.

Akwa Ibom na daya daga cikin jihohin kudancin Najeriya inda ake kaiwa jami’an tsaro a watannin baya-bayan nan.

Hare-haren sunyi sanadin salwantar rayyukan jami’an tsaro 11 a cikin watanni uku da suka gabata.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, Bernard Onyeuko, mukadashin direktan, sashin watsa labarai na sojoji, ya ce sojoji sun fara yi wa miyagun dauki dai-dai.

Ya sanar da hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan rundunar daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yuni.

Onyeuko ya ce, “bayyanan sirri masu inganci sun bawa sojoji damar kamo mambobin IPOB/ESN” wadanda aka ce sune suke kai wa jami’an tsaro hare-hare a jihar.

“Sojoji a Ikot Ekpene sun kama wasu mambobin IPOB/ESN a karamar hukumar Essien Udim a Akwa Ibom bayan samun bayannan sirri kan ayyukansu a yankin,” in ji kakakin na sojoji.

“Wadanda ake zargin suna daga cikin mambobin IPOB/ESN da ke da hannu wurin kisa da kona yan sanda da ofisoshin yan sanda a yankin.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here