Gwamnan Bauchi Ya Sauke Dukkan Kwamishinonin Sa

0
182

Daga Rabo Haladu.

GWAMNAN Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya sauke dukkan kwamishinonin sa baki daya.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai, Muktar Gidado ya shaida aika wa yan jaridu a ranar Laraba, ya bayyana sallamar “dukkan Kwamishinoni tare da rushe Majalisar Zartaswar Jihar Bauchi da sauran masu rike da mukaman siyasa da su ka hada da Sakataren Gwamnati, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, har da dukkan Mashawartan Musamman.”

Sanarwar ta “tsame sunayen mutum hudu wadanda sallamar ba ta shafa ba.”

Babu dai wani dalilin sallamar a cikin sanarwar wadda ta hada da cewa kowane kwamishina ya damka harkokin ofis a hannun Babban Sakataren Ma’aikatar sa.

Bala Mohammed wanda dan jam’iyyar PDP ne, ya gode wa dukkan wadanda ya sallamar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here