Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Sheƙe Sufetan Ofishin

0
301

Daga Usman Nasidi.

WASU yan bindiga aƙalla 15 sun kai hari ofishin yan sanda dake Ojoto, karamar hukumar Idemili ta kudu, jihar Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun hallaka sufetan caji ofis ɗin a yayin harin.

Wata majiya a yankin da abun ya faru ta bayyana cewa jami’an tsaron dake bakin aiki sun maida martani ga yan bindigan, inda akai ɗauki ba daɗi tsakaninsu.

“Yan bindigan na zuwa suka buɗe wuta amma jami’an yan sanda suka maida martani, maharam sun zo a motar Sienna guda biyu .” inji majiyar.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, yace bayason magana akan lamarin har sai bayan ya ziyarci ofishin.

“Ina shirin zuwa wurin, a halin yanzun ba zance komai har sai bayan naje wurin da abun ya faru.” inji Tochukwu.

Amma wani babban jami’in ɗan sanda a jihar wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da kai harin.

Yace: “An kashe mana sufetan yanki yau. Kwamishinan yan sanda, Chris Owolabi, ya shirya kai ziyara yankin.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here