Dokta Wailare Ya Gamsu Da Yadda APC Ke Bunkasa A Jihar Kano

  0
  340

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

  JIGO a jam’iyyar APC daga mazabar tarayya ta Dambatta da Makoda Dokta Saleh Musa Wailare ya nuna gamsuwar sa bisa yadda jam’iyyar take kara samun magoya baya a dukkan fadin kasarnan.

  Yayi wannan tsokaci ne a sakon da ya fitar dangane da yadda jam’iyyar ta APC take ta karbar magoya baya wanda a cewar sa, hakan ya nunar da irin nasarorin da take samu tun lokacin da ta karbe ragamar mulkin kasa a shekara ta 2015.

  Dokta Wailare ya kuma sanar da cewa wannan hali na ci gaba da jam’iyyar APC ke ciki ya nunar da cewa al’umar Nijeriya sun gamsu da yadda take mulki a dukkanin matakai uku na gwamnati, sannan na bayyana cewa APC itace kadai jam’iyya a kasarnan da take da manufofi na ciyar da kasa gaba ta kowane fanni.

  ” inaso inyi amfani da wannan dama domin taya murna ga jam’iyya mu ta APC a mataki na kasa da jihohi da kananan hukumomi har ma da mazabu saboda yadda jam’iyya mu ke samun ci gaba duba da yadda kowa ya gamsu da yadda take jagorancin kasar nan, sannan ina taya murna ga maigirma gwamna jihar zmfara Matawalle da Malam Salihu Sagir Takai da A.A. Zaura da suka canza sheka zuwa jam’iyya mai kishin al’uma “. Inji Wailare.

  A karshe, matashin dan siyasar kuma wanda yake bada gagarumar gudummawa wajen ci gaban jam’iyyar ta APC a kananan hukumomin Dambatta da Makoda Dokta Saleh Musa Wailare ya jinjinawa gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda jagoranci na adalci da yake yiwa al’umar jihar Kano batare da nuna gajiyawa ba.

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here