Shell Zai Biya ‘Yan Yankin Ogoni Tarar Naira Biliyan 45

0
266

Daga Wakilinmu

Katafaren kamfanin man fetur na Shell Petroleum Development Company ya amince ya biya naira biliyan 45 ga mazauna Ogoni na Jihar Rivers da ke yankin Neja-Delta a kudancin Najeriya.

Mazauna Ƙaramar Hukumar Ejama-Ebubu waɗanda lauya Isaac Agbara ya wakilta tare da wasu tara, sun shigar da ƙarar ce shekara 32 da suka wuce suna neman a biya su fansar lalata musu ƙasa da Shell ya yi saboda kwararar mai.

Tun a 2010 wata Babbar Kotun Tarayya a Najeriya ta umarci a biya su fansar amma aka yi ta ɗaukaka ƙarar har zuwa Kotun Ƙoli.

Kotun Ƙolin ta tabbatar da hukuncin a 2019, sai dai kamfanin na ƙasar Netherlands ya ci gaba da neman yadda zai guje wa biyan kuɗin kafin daga baya ya sake dawo da ƙarar Babbar Kotu Tarayya a Abuja.

Shell ya bayyana aniyarsa ta biyan kuɗin ta bakin lauyansa Aham Ejelamo yayin zaman kotun na ranar Laraba.

Mista Ejelamo ya ce ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar matakin biyan kuɗin ne tun kafin zaman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here