Gidauniyar Tamallan Za Ta Horar Da Mutane 300 Ilimin Fasahar Sadarwa.

0
268
JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
GIDAUNIYAR Tamallan, watau (Tamallan Foundation) za ta ba da horo kan ilimin Fasahar Sadarwa ta zamani wanda  aka fi sani da “Information Technology” ta yadda al’umomin Dambatta da Makoda za su ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen rabauta da ilimin Sadarwa kamar yadda ake bukata.
An shirya bada horon ne bayan kammala dukkanin tantance wadanda suka cike takardun neman shiga shirin wadanda Kuma aka zakulo daga mazabu 22 na kananan hukumomin Dambatta da Makoda da kuma wadanda  da aka zabo daga  sauran bangarori domin ganin an taba kowane bangare na rukunin al’umar mazabar ta Dambatta da Makoda.
Wakilinmu ya yi kokari wajen jin ta bakin Shugaban gidauniyar Tamallan, watau Dokta Saleh Musa Wailare domin samun  Karin haske dangane da wannan Kokari, inda Shugaban gidauniyar ya bayyana cewa ” Babban burin mu shine muga mun kawo abubuwa na alheri a kananan hukumomin Dambatta da Makoda musamman abubuwa da zasu amfani yankin, don haka da yardar Allah wannan gidauniyar zata ci  gaba da taba kowane bangare na zamantakewar al’uma batare da nuna wani bambancin siyasa ko na ra’ayi ba” Inji shi.
Suma wasu matasa Malam Adam Sani daga More da Musa Aminu daga garin Galoru sun sanar da cewa ko shakka babu abubuwa alheri da Dokta Saleh Musa Wailare yake yi a wannan yanki suna Kara wa al’uma wayewa da sanin hakkin Kai da Kuma sanin su waye shugabanni da ake bukata musamman a tsarin da ake ciki na dimokuradiyya, tareda yin godiya ga gidauniyar Tamallan saboda wannan tunani na bada horo kan fasahar sadarwa wadda duniya ke alfahri da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here