KADPOLY: Ya Kamata A Yi Dokar Samar Da Digiri Na Farko Zuwa Na 3 – Hon Abba Anas

0
257
Usman Nasidi, Daga Kaduna.
SHUGABAN Kungiyar tsofaffin Ɗaliban Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Tarayya (KADPOLY) da ke Kaduna, Honarabul Abba Anas Adamu ya buƙaci a samar da Dokar da za ta bai wa al’umma damar yin karatun Digiri na farko zuwa na uku domin kara inganta harkokin Kwalejin.
Da yake jawabi yayin Kaddamar da wasu kwamitin Kungiyar ta (KADPOLY) wanda ya gudana a dakin taro na Hadi Auwal dake cikin Kwalejin ranar alhamis a garin Kaduna, shugaban ya bayyana cewa ya na da matukar fa’ida a samawa Kwalejin damar da zata bunkasa al’umma da kanta ta fannin ci gaaba.
Ya kara da akalla makarantar ta kai shekaru 66 da kafawa kuma ta yaye wasu manya-manyan mutanen da ke da iko a kasar nan ciki har da mayan yan Siyasa, yan Kasuwa da wasu da suka zama farfesoshi ta hanyar tallafawar ta don yin haakan wani babban matakin nasara ne ga Kwalejin da al’ummarta.
Ya ce “wannan kwamitocin da aka Kaddamar, an Kafa su domin kara janyo matakin nasara da cigaban al’umma da Makarantar ita kan ta, don haka ake saran kowace kwamitin za ta yi aiki tukuru wajen ganin an cimma matakin nasara da kawo sauyi mai Inganci a cikin tsarin gudanar da harkokin Makarantar.”
“Kungiyar tsofaffin Ɗaliban za ta Iya kasancewa da kwarin gwiwa ne idan ya zamana ta na da zakakurin mutane a matsayin mambobinta, kuma duk yadda aka yi idan suka nisanta kansu da juna, toh zasu dakushe hasken wannan Kwalejin wanda Kungiyar tasha alwashin ganin ta zama abun alfahari a gare ta don kawa mata cigaba.”
“Ina alfaharin sanar daku cewa muna Ƙoƙarin ganin cewa an samu wata kyakkyawar alaka tsakanin mu da hukumar zartarwar makarantar wajen ganin cewa an samu nasara a kan matsaloli da ke addabar Kwalejin ta mu domin yayin da Kungiyar ta yi kokarin gano matsalolin dake tattare da Kwalejin hukumar makarantar ce ta taimaka a kan hakan.”
“Saboda haka a bada dama wannan makaranta ta rika gudanar da Digiri na farko zuwa na uku amma ba za a rushe abin da muke da shi ba, domin Kwalejin ta kara bunkasa saboda mafi yawancin mutanen da makarantar ta horar kan guje mata daga karshe bayan ta gama daukar dawainiyarsu wajen gina su, toh amma babu halin da ita zata amfana dasu.”
“Bai kamata a ce a iya shekarun da Kwalejin ta yi ace ba irin wadannan damar a tattare da ita ba, amma sai ka ga makarantun da basu waci shekaru biyar zuwa goma ba, suke cin gajiyar wannan damar da take da bukata kana da amfani da mutanen da ta horar kuma ta wahala a kansu, wanda ko a yanzu Kwalejin tana kawance da wasu Jami’o’in da take bayar da takardun shaidar Digiri din amma da sunan Jami’o’in.
A nashi Jawabin, Mukaddashin shugaban Kwalejin (KADPOLY), Dakta Suleman Umar, ya bayyana cewa Kwalejin ta na tsimayen jiran hanyoyin da zata taimakawa Kungiyar wajen ganin ta bunkasa, kana ta hada kai da hukumar zartarwar Kwalejin domin ganin ta kai ga matakin nasara.
Daraktan Harkokin ci gaba na Kwalejin Lawal Anako Opoty da ya wakilci shugaban Kwalejin, ya ta ya mambobin kwamitin Kungiyar da aka Kaddamar murna da fatan alheri, kana ya kara da yi musu tunin cewa wannan wani wani nauyi ne aka dora musu na ganin cewa sun yiwa al’umma aiki ta hanyar da ya dace domin sauki nauyin da ke kansu.
Kwamitocin da aka Kaddamar sun hada da kwamitin Kudi da duk wasu harkoki, kwamitin bincike da ci gaba, Kwamitin sadarwa da membobi, kwamitin hulda da kasashen waje, kwamitin horo, da wasu sauran kwamitin masu mahimmaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here