LITTAFI KAN ZAKKAH  

0
431
SP. Imam Ahmad Adam Kutubi

DAGA SP. IMAM AHMAD ADAM KUTUBI

ZONE 7 POLICE COMMAND HEADQUARTERS,

FCT ABUJA.

08036095723

ABUBUWAN DA KE CIKI

1. WADANDA ZAKKA YA WAJABA A KANSU

2. ZAKKAR DABBOBI

3. ZAKKAR RAKUMA

4. ZAKKAR SHANU

5. ZAKKAR TUMAKI DA AWAKI

6. ZAKKAR ABINCI

7. ZAKKAR KUDI

8. ZAKKAR KADARA

9. WADANDA AKE BAWA ZAKKA; FAKIRI, MISKINI, MAI TARA ZAKKA, KAFIRIN DA AKE KWADAIYIN MUSULUNCINSA, SAI YANTA BAWA, MAI BASHI A KANSA, HANYAR DAGA ADDININ MUSULUNCI FISABILILLAHI (DA’AH), MATAFIYI. 3

ZAKKAH

Zakkah itace wani mikdari na dukiya da aka iyakanta, wanda ake fitarwa daga dukiya kebantacciya, a cikin lokaci kayyadadde.

Fitar da zakka farillane, tana daga cikin shikashikan musuluncin nan biyar. Duk wanda yakinya fitar da ita sarki zai karbeta daga gare shi da karfi. Zakkar kuwa tayi. Zakka bata wajaba akan mutum sai sharuda shida sun tabbata a gareshi.

1. Musulunci, wajibi ne musulmi ya fidda zakka daga dukiyarsa. Ko da kiwa jinjiri ne ko mahaukaci. Fitar da ita yana kan waliyyin yaron ko mahaukacin.

2. Zama da. Babu zakka a cikin dukiyar bawa. Amma idan aka yanta shi, alhali yana da dukiya, zai fara lissafi da ranar da aka yanta shi, ya fitar mata zakka, idam shekara ta kewayo.

3. Nisabi. Zakka ba ta wajaba akan mutum sai yawan dukiyarsa ta kai nisabi (Akallan abinda ya isa a fitar da zakka dashi).

4. Mallaka. Wajibine dukiyar da ta ke ga hannun mutum ta zama mallakinsa ne. Saboda haka babu zakka akan wanda aka ba ajiyar dukiya, wanda ya karbi jingima da wanda yayi tsintuwa.

5. Cikar shekara. Ba zakka akan mutum sai dukiyarsa ta cika shekara a hannunsa, idan kudine ko dabba. Farkon shekara shine ranar da mutum ya samu kudi na gado, ko kyauta, ko ranar da ya samu jari, ko dabbobi. Ribar kudi da yayan dabbobi suna bin shekarun asalinsu. Kuma an

4

shardanta game da cikar shekara dabbobi zuwan sa’i wurin mai garke. Sa’i shine wanda sarki ya nada don karban zakkar dabbobi daga masu su. Idan mutum ya fitar gabannin zuwan sa’i babu zakkarsa. Saidai idan babu sa’i a kasar, ko kuma yayi jinkirin zuwa karbanta, bada wani uzuri ba. Amma ita zakkar abinci tana wajaba a lokacin da abinci ya nuna. A wani kauli kuwa ance a ranar da aka girbe shi.

6. Rashin bashi. Babu zakkar kudi akan wanda ake bi bashi. Wato idan bashin da ke kansa da a ce ya biyashi ne, kudin da zai ragu a hannunsa zai kasa nisabi, to babu zakka a kansa. Sai fa idan yana da wata dukiya wanda ya ajiye don bukatar kansa, kamar tufafi da gidaje da gonaki da dabbobin da basu isa zakka ba, wanda sune kudinsu zai iya biyan bashinsa, to a wannan hali zakkar kudi ta wajaba a kansa. Bashi ba zai hana fitar sda zakkar abinci ba sa dabbobi ba. Haka kuma zakka bata inganta sai da abu hudu

✓ Yin niyya. Wajibi ne mutum yayi niyya a zuciyarsa lokacin da yake fitar da zakka, ko lokacin da yake bada ita ga matalauta, cewa ita zakkace. Amma fa ba ana nufin ya fadawa mutum cewa zakka ne ya bashi ba. A’a wannan makruhi ne. Idan mutum yayi niyyar kyauta ko sadaka ta son rai zakka batayi ba.

✓ Wajibi ne a raba zakka ga matalautan wurin da ta wajaba, ko ga matalautan da ke kusa da wurin, wadanda nisansu bai kai mil 48 ba. Gurin da zakkar abinci ta wajaba shine gurin da gona take, dabbobi kuwa inda aka samesu, kudi kuwa garin da mai su

5

yake. Amma ya halatta a dauki zakka a kaita guri mai nisa fiye da mil 48, da shaeadin talaucin matalautan can ya fi na matalautan wurin da ta wajaba tsanani. Amma a kowane hali za a rage wa matalautan wurin da ta wajaba, wani abu daga cikinta.

✓ Jiran cikar shekara. Wajibi ne a dakata kada a fitar da zakka sai shekara ta cika.

✓ Wajibi ne mutum ya bayar da zakka ga irin mutanen da shari’a ta ce a bawa. Su ne mutane iri takwas da aka zanta a cikin alqur’ani sura ta tara aya ta 60:

Fakiri, shine wanda bai mallaki abincin shekara ba.

 Miskini, shi ne wanda bai mallaki abincin kwana daya ba.

 Mai aiki game da zakka, za a ba da zakka ga mai aiki game da ita ko da kuwa mawadaci ne. Misali kuwa shine kamar mai karbota daga hannun mutane da mai rubutu, da manzon da a ke aikawa don tattaro masu bada zakka.

Kafirin da ake kwadaitarwa. Ana ba kafiri zakka da sharadin ya zama an bashi itane don a kwadaitar da shi ga shiga musulunci, ko kuwa don shi sabon shiga musulunci ne, ana son a kara tabbatar da zuciyarsa a ciki.

Yanta bawa, ana sayen bawa ko baiwa da dukiyar zakka a yanta su da sharadin su zama musulmi ne.

6

Mai bashi a kansa. Ana ba da zakka ga mutum mai bashin da baya da abin da zai biya shi da shi, da sharadin ya kasan ce shi da ne, musulmi, kuma yaci bashin nan domin larura wanda bata fasadi na.

Hanyar alheri ta Allah. Ana ba da zakka ga hanyar alheri ta Allah. Kamar bada ita ga mayaki ko jihadi, da sayen kayan yakin jihadi, da ba malaman fikhu da limamai da alkalai idan ba su da albashi daga baitil-mali.

Matafiyi. Ana bada zakka ga bako ko matafiyi wanda guzurinsa ya kare.

Idan mutum ya bada zakka ba ga dayan wadannan ba, babu zakkarsa, saboda haka sai ya je ya karbo ta daga gare shi ya bada ita ga wanda ya cancanta.

ZAKKAR DABBOBI

Dabbobi da ake fitar wa zakka su ne rakuma, da shanu, da tumaki, da awaki kadai. Babu zakka a cikin wanin wadannan dabbobi.

RAKUMA

Babu zakka ga rakuma sai yawansu ya kai biyar, wato shi ne nisabinsu. Daga rakuma biyar zuwa tara, za’a bada tinkiya daya, ko akuya. Daga rakuma goma zuwa sha 14, za a bada tumaki biyu. Daga 15 zuwa 19, za a bada tumaki uku, daga 20 zuwa 24, za a bada tumaki hudu. Daga rakuma 25 zuwa 35 za’a bada rakuma mace mai shekara biyu da haihuwa. Daga rakuma 36 zuwa 45 za a bada rakuma mace mai 7

shekara uku. Daga 46 zuwa 60 za a bada rakuma mai shekara hudu, daga 61 zuwa 75 za a bada rakuma mai shekara biyar, daga 76 zuwa 90 za a bada rakuma biyu masu shekara uku uku. Daga 91 zuwa 120 za a bada rakuma biyu masu shekara hurhudu. To abinda ya shige haka sa a duba a gani, a cikin kowace arba’in a ba da rakuma mai shekara uku, a cikin kowace hamsin kuwa a bada rakuma mai shekara hudu.

SHANU

Babu zakka a cikin shanu sai sun kai talatin, wato shine nisabinsu.

Daga saniya 30 zuwa 39, za a bada makara ko maraki mai shekara uku, daga 40 zuwa 59 za a bada saniya mace mai shekara hudu. To abin da ya shige haka sai ko wace talatin a fitar da maraki ko maraka, mai shekara uku, ko wace arba’in kuwa sai a bada saniya mai shekara hudu.

TUMAKI DA AWAKI

Tumaki da awaki an dauke su abu guma. Idan dukiyar mutum tumaki da wakice sai ya lissafa su kamar duk jinsi daya ne. A yanzu zan yi amfani da kalmar tumaki a matsayin su duka. Babu zakka ga tumaki sai yawansu ya kai arba’in wato shi ne nisabinsu.

Daga tumaki 40 zuwa 120 za a bada tinkiya daya, ga 121 zuwa 200 za a bada tumaki biyu, daga 201 zuwa 399 za a bada tumaki uku. To abin da ya shige haka a cikin kowacce dari za’a fitar da tinkiya daya. Duk wurin da akace a bada tinkiya, ko kuwa a wajenda zakkar rakuma ce, to, ya halatta a bada akuya ko rago ko bunsuru. Wajibi ne shekarun abin 8

da za’a bayar ya kai shekara daya. A wani kauli kuwa an ce har mai wata shida zai isa.

ZAKKAR ABINCI

Abincin da ake fitar wa zakka naui ishirin ne kadai, zan rubuta su da sunayensu na larabci domin yawancinsu ba mu da su a kasar nan.

MASU KWAYA

Kamhu = Alkama

Sultu = Alkama

Sha’ir = Alkama

Urzun = Shinkafa

Duhnun = Gero

Zaratun = Dawa

Alasun

KADANI (MASU DADEWA KAMIN SU TSIRO)

Adasu (lentis)

Lubiya= wake (haricot beans)

 Falu (horse beans, broad beans, peanut)

Himmasu (chick peas)

Turmus (lupine)

Basilah (pea, french pea)

Julban (Marrow fat)

MASU MAI

 Kurdum

Habbul-fijlil-ahmar (Radish)

9

Simsim = Ridi (Sesame)

Zaitun (Olive)

Tamrun = Dabino

Zabib = Inabi.

Dangoginnan na alkama uku an dauke su a kan jinsi daya. Saboda haka idan mutum ya shuka nau’i biyu ko duka uku, idan amfanin da ya samu daga garesu gaba daya ya kai nisabi, zai fitar da zakka. Haka kuma dangogin kadanin nan bakwai su ma an dauke su a kan jinsi daya. Sauran ragowar kuwa ko wannensu jinsin kansa ne ba a hada shi da wani. Idan bai kai nisabi ba shi kadai, babu zakka a cikinsa. Nisabin abinci shine buhu biyar, kowanne buhu sa’i sittin. Wayo nisabi dai shi ne sa’i dari uku. Kowane sa’i kuwa yawansa mudu hudu, yawan mudu shine gwargwadon abin da zai cika hannuwan mutum matsakaici, bayan ya hadasu wuri daya, bai bude su ba, kuma shi bai matsesu ba. Ana kula da yawan nisabi bayan an shire kaikayi da dukkan abincin daga alada ba a kan ajiye shi da kaikayi ba. Kaikayin shinkafa da na alasu ana shigar dashi cikin lissafi.

Zakkar da za a fitar daga cikin abinci shine ushurin abin da mutum ya samu idan da ruwan sama ko malali aka shayar da shi. Idan kuwa an shayar dashi ne da ban ruwa, za’a fitar masa da ushuri. Wato kashi daya daga cikin ishirin. Za a fitar da zakkar nan daga cikin asalin nau’i abinci da mutum yayi, sai dai idan nau’in abincin nan yana daga cikin masu mai, to anan kan za’a fitar daga mansa. Sai fa kuwa idan nauin abinci ba irin mai bushewa bane anan kuma za a fitar da zakkar kudin siyar dashi wato a bada ushurinsu idan kuma ba a siyar dashi ba sai a bada ushurin kimarsa. Idan kuma abincin mai 10

bushewa ne za a fitar da zakkar nan daga cikin kudin da aka siyar dashi. Wato a bada ushurinsu. Idan kuwa ba a siyar da shi ba, sai a bada ushurin kimarsa.

ZAKKAR KUDI

Abinda ake nufi da kudi a nan shine zinariya da azurfa. Kudin da akayi da zinariya ana kiransa dinari, wanda kuma akayi da azurfa, ana kiransa dirhami. Dukkan dukiyar ciniki wanda ba zinariya ko azurfa ba ana kiranta kadara. Zinariya da azurfa an dauke su jinsi daya. Wato ana lissafasu a game don a samu cikar nisabi.

Nisabin zinariya shi ne ta kai dinari ashirin. Nisabin azurfa kuma shine ta kai durhami dari biyu. Wato kowanne dinari guda canjinsa dirhami goma ne a cikin babin zakka. Wanda ya mallaki dinari goma da dirhami dari, ga misali, zai hadasu ya fitar da zakkah.

To, da yake da dinari ne ko dirhami a ke kimanta ko wacce kadara don a fitar mata da zakka, don haka sai sharia ta kayyade nauyin ko wane daya daga cikinsu, domin kada rudewa ta auku a lokacin da aka rasa kudi na dinari ko dirhami, na sharia. Yadda sharia ta yanke shi ne, nauyin dinari yana daidai da nauyin kwaya 72 ta alkamar sha’ir matsakaici bayan bushewarta. Nauyin dirhami kuwa yana daidai da nauyin kwaya 50 ta alkamar sha’ir. Saboda haka duk kudin da aka kera da wani karfe daban za a kimanta shi da dinari ko dirhami. Wato gwargwadon yawan kudin da zai iya sayen zinariya mai nauyin dinari ashirin, ko azurfa mai 11

nauyin dirhami, a zamanin da ake a ciki, shine nisabin irin kudin nan.

Abin da mutum zai bayar idan dukiyarsa ta kai nisabi shi ne rubu’in ushurinta. Wato kashi daya daga cikin arbain. Idan mutum yana da zinariya ko azurfa a dunkule ba a kera ta kudi ba, zai fitar da zakkar nauyinta ko wace shekara. Sai dai idan kayan adone wanda sharia ta halatta a yi amfani da shi. Kamar dutsen wuya da yankunne da munduwa, da zobe da dan hanci da hakori da gidan alqurani, da kuben takwabin yin jihadi. Amma idan yanayin haya ne da kayan nan na ado na zinariya ko azurfa, to, zai fitar musu da zakka kowace shekara. Kamar yadda zai fitar musu da zakka idan ya ajiye su ne don tanadin gaba, ko da talauci zai auko masa.

Babu zakka a cikin kadara wanda bata ciniki ba, kamar bayi, da dawaki, da jakuna, da dabbobin da ake fitar wa zakka da abinci, wanda suka kasa nisabi, da gidaje, da gonaki, da tufafi. Babu zakka akan mutum idan ya mallaki dayan wadannan abubuwa da niyyar bukatar kansa kawai. Amma idan da niyyar ciniki ne, to wajibine ya fitar musu da zakka kowace shekara.

ZAKKAR KADARA

Mai kadara yana da hali biyu, na farko, ko dai ya zama mai ihtikari ne. Wato shine mai rike kadarar sa, bazai sayar da ita ba, komai yawan shekarunta, sai ranar da kasuwan irin wannan kadarar ta tashi, ya ga zai samu babbar riba. To shi irin wannan mutum zai fitar da zakkar kadararsa duk randa ya sayar da ita, idan da sharadin kudinta ya kai nisabi. Zai 12

fitar mata da zakkar shekara guda, ko da kuwa ta dade a ajiye tayi shekaru masu yawa kafin ya siyar da ita. Hali na biyu kuma, ko ya zamo mai juyawar kadararsa ne, wato da ya sayi kadarar sai ya siyar da ita yadda kasuwa ta kawo, ya kuma sake siyan wata, to shi irin wannan mutum kowace shekara zai kimanta duka kadarar dake gareshi sannan ya hadata da tsabar kudin da ke hannunsa a lokacin nan, ya fitar musu da zakka gaba daya.

SAURAN MAGANGANU

Mutum ba zai bada zakka ga wanda sharia ta wajabta masa ya ciyar da shi ba. Kamar bada zakka ga matar mutum, ko yayaynsa wanda basu balaga ba, da iyayensa matalauta, da bayinsa. Amma ya halatta ga mata tabawa mijinta matalauci zakka.

Amma wani kauli kuwa ance makhruhi ne ta bashi zakkah.

Ba a bawa zuri’ar bani hashim zakkah. Hashim shine kaka na biyu ga Annabi Muhammad S.A.W. (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Mai talauci daga zuriar bani hashim za’a bashi kudi daga baitil mali. Idan kuma basu samu daga baitil mali ba, har kuma ya zamana suna da talauci, to, sun fi kowa cancantar a bawa zakka, kamar yadda mafi tsananin talauci ya fi mai saukin talauci a bashi zakka. Ya halatta ga mutum ya kaiwa sarki adali zakkarsa don a bawa mutanen da suka cancanta a bawa. Amma idan ba adali bane bai kamata akai masa zakkar nan dan ya rabawa matalauta ba. Idan kuma har mutum ya kai masa bisa ga son ransa to babu zakkarsa. Idan mutum ya bada kimar abinda 13

ya wajaba ya fitar na zakka, zakka tayi kyau game da karhanci, amma idan an tilasta shine kan ya bada kimarsa to ta isar masa babu wani karhanci.

A wajen bayar da zakka mutum zai bayar daga mutawassidin dukiyarsa. Ba za a karbi nakasassa ba. Kuma ba za a tilasta masa don ya bayar daga zababbiyar dukiyarsa ba. Saboda haka baza a karbi dabba wanda ta kasa shekarun zakka ba, ko tsohuw ko mai ciki, ko karo ko turkakkiya. Amma ya halatta ga mai dukiya ya bada zakka daga zababbiyar dukiyarsa da son ransa.

Idan mutum yazo fitar wa dukiyarsa zakka, ba zai fitar wa bashin da yake bin wani ba, zai bari har sai ranar da ya karbe shi, sannan ya fitar mata da zakka na shekara daya kadai. Koda kuwa yayi shekaru da yawa kafin ya karbe shi. Sai dai kawai idan yaki karba ne don gudun zakka. Idan kuwa hakane, to, ranar da duk y karba zai fitar mata da zakka har da na shekarun baya da suka wuce dukansu.

Idan mutum ya hako zinariya ko azurfa daga ma’adinansu, idan abin da ya samu ya kai nisabi, to, zai fitar masa da zakkar rubu’in ushurin, a ranar da ya hako shi. Ba maganar cikar shekara anan. Hukuncin ma’adinai yana cikin hannun babban basaraken kasa. Babu zakka ga sauran abubuwan da ake hakowa daga ma’adinansu ban da zinariya da azurfa. Lallai ne a fitar da zakka saboda wanda baya fitar da zakka yana cikin mushirikai ko da yana sallah kuma yana azumi saboda Allah ya ce; wadanda suke tara dukiya, zinari da azurfa sannan basa ciyar da ita saboda da ga addinin Allah, to, ayi musu albishir da azaba mai radadi, to ranar tashin alkiyama za a narkata adinga yi musu lalas da ita a goshinsu 14

da kwibinsun na dama da na hagu, da kuma bayansu ana ce musu wannan itace kudinda kuka tara a duniya kukaqi cire zakka. Don haka kudandani azabar abinda kuka boye a bankuna kukaqi bada zakkar su. Wato masu ajiye kudi a banki ko a wuraren ajiye ajiyensu amma basa fitar musu zakkah. An samu wani mutum ya rasu bayan an birne shi a kabarinsa bayan duk mutane sun tafi, sai dan uwansa ya tsaya yanayi masa addua, yana cewa idan mai laifi ne Allah ka yafe mass kurakurensa, ka wanke shi kamar yadda ake wanke farar tufafi, ka rabashi da azabar kabari da wutar jahannama. Sai wannan dan uwan nasa yaji yana ihu, wayyo a tsirar dani, na halaka. Da dan uwansa yaji haka sai ya tone kabarin dan ya cire shi, sai ya ganshi a daure da sarkoki, sai yaje cire sarkan sai wuta ta konashi sai ya mayar da kasan kabarin ya rufe, sai ya tafi wajen wani sahabi ana kiransa abu zarrin. Sai yace ya abu zarrin yanzu daga wajen bisan dan uwana muke bayan birne shi kowaya ya watse sai na tsaya inayi masa addua, sai naji yanata ihu, natona kabari na cire shi sai na kone a hannuna. Sai abu zarrin yace mai dan uwanka yake a duniya haka sai yace dan uwana yana sallah yana azumi amma baya cire zakkar duniyarsa. Sai yace to dan uwanka yana cikin azaba na kabari. Saboda Allah yace; kada wadanda Allah ya basu dukiya basa cire zakka suyi zaton alkhairi ne agare su, a’a sharri ne a garesu sbd ranar da kona abinda suka tara a duniya a dinga goga musu a fuskokinsu da kumatunsu da kwibinsu na hagu da dama da kuma bayansu, ana cewa kudandani azabar kudin da kika tara kukaqi ciree zakka a duniya. To wannan yana nuna mana lallai akwai azaba mai tsanani ranar tashun alkiyama ga duk wani mai kudin da yaki cire zakka, ko ta kudi, ko na 15

amfanin gona, ko na dabbobi, ko na kadarori na saye da siyarwa da yake ciniki da su kuma baya fitar da zakka. Kuma Allah yace hakika tsananin azaba ya tabbata ga mushirikai wadanda basa fitar da zakka, su iri wadannan mutane a ranar rahira kafirai ne. To kunga hatsarin abin qur’ani ya baiyyana wanda baya fitar da zakka kafirine ko mushiriki koda yana azumi da sallah da sauran ibadu amma baya zakka to yana cikin azaba ranar lahira. Allah ya tsare mu. Amin.

ZAKKAR FID DA KAI

Fid da kai sunnah ce mai karfi. Tana wajaba akan kowane musulmi, babba da yaro, mace da namiji, da ko bawa, da sharadin akalli sa’i guda ya ragu daga cikin abincin da mutum ya mallaka a ranar da ta wajaba a kansa. Yawanta sa’i guda ne kan kowane mutum. Lokacin da take wajaba akan mutum shine faduwar rana a yinin karshe na ramadan. A wani kauli kuwa ance bata wajaba sai da alfijirin ranar sallah. Amma dai a kowane hali mustahabbi ne ayi saurin fitar da ita da fitowar alfijirin ranar sallah. Ana bayar da ita ga musulmi fakiri ko miskini kadai. Ba a bayar da ita ga bawa ko kafiri ko mawadaci. Mutum shi zai fitar da zakkar nan ga wanda duk ya ciyar da shi ta wajaba akansa da sababin zumunta ko aure ko bauta.

Idan ta wajaba akan mutum amma yayi jinkirin fitar da ita, to, bata faduwa a kansa, saboda da haka zai fitar da ita ko bayan watanni masu yawa.

Bai halatta a fitar da ita ba sai daga dayan nau’u’ukan abincin nan goma. 16

1. Kamhu

2. Sha’ir

3. Sultu

4. Dabino

5. Zabib

6. Cukui

7. Gero

8. Dawa

9. Shinkafa

10. Alasu

Amma idan an rasa ko da daya daga cikin wadannan abubuwa, to, ya halatta a fitar da zakka daga cikin irin abincin da mutanen gurin suke ci.

DUK MAI SON KARIN BAYANI YA DUBA LITTAFIN ALKALIN ALKALAI ALHAJI HALIRU BINJI. A CIKIN LITTAFINSA MAI SUNA IBADA DA HUKUNCI LITTAFI NA BIYU. ALLAH YA JIKANSA YA GAFARTA MASA DAMU DA IYAYENMU DA ZURI’ARMU BAKI DAYA. AMIN

DAGA SP. IMAM AHMAD ADAM KUTUBI

ZONE 7 POLICE COMMAND HEADQUARTERS,

FCT ABUJA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here