MUSA MUHD. KUTAMA Daga Kalaba
WATA baiwar Allah mai Suna Hajiya Hauwa Abubakar Bichi Mai fafutukar Kare hakkin mata ta bukaci a rika tausayawa matan da kananan yaran da masu kama mutane Suna Garkuwa dasu domin Neman kudin fansa suka kama ko kashe mazajen su.
Hajiya Hauwa Abubakar Bichi ta bukaci haka zantawar su da wakilin mu a Kalaba .Ta ce “Halin da maya da kananan yara da aka sace iyayen su maza ko kuma suke yin gudun hijira a wurare daban-daban na Jihohin Arewa maso Yamma Ina tausaya musu kuma abin tausayi ne ya kamata a tausaya musu ya kamata kuma gwamnati ya dubi dumarin mutanen” inji ta
Taci gaba da cewa tana yin kira ga sauran Al’umma a taimaka wa wadannan mutane”.
Kazalika Mai fafutukar hakkin matan ta kara da cewa bai kamata ba a bar su kara zube , ba ko kyale su babu wata mahimmiyar kulawa ba musamman yadda a wasu Jihohin ake fama da cutar Amai da Gudawa ba .
Ta ce gwamnati ke da hakkin samar musu da makarantun Boko da na Islamiyya
Karshe ta yi fata hukuma za ta ci gaba da yin nazarin halayen da maya da qananan yara da Yan bindiga suka Jefa iyayen su maya ciki.