Gwamna Malam Nasiru El- Rufa’i Adalin Mutum Ne – Mamadi

0
178
Mustapha Imrana Abdullahi
HONORABUL Abubakar Mamadi daga karamar hukumar Igabi, ya bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da cewa mutum ne da ke son yi wa kowa adalci domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Abubakar Mamadi ya bayyana hakan ne lokacin da yake yi wa ‘ya’yan jam’iyyar APC jawabi a wajen wani babban taron da ya kira a Kaduna.
Abubakar Mamadi, ya ce babban dalilin da ya sa muka kira wannan taron shi ne a gaya wa kowa irin halin da ake ciki game da lamarin APC a karamar hukumar Igabi, shi ne
” Mai girma Gwamna mai adalci Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, ya ce kowa ce karamar hukuma ta tabbatar an yi wa dukkan dan jam’iyya adalci a cikin APC, wato kowa ya bi ka’idar da jam’iyya ta shimfida ba maganar son rai a cikin harkokin jam’iyya, don haka muka ga ya dace a tara jama’a domin duk mai hakki a ba shi hakkinsa kamar yadda doka da ka’ida suka tanadar”.
Don haka ina mai tabbatar maku cewa Gwamna ya bayar da umarnin cewa a je a yi aiki da dukkan ka’idojin da doka ta tanada ta yadda za a yi wa kowa adalci a dukkan al’amura.
A wajen taron masu ruwa da tsakin akwai tsohon dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Igabi Barista Ibrahim Bello Rigachikun kuma duk sun shaida wa taron irin aniyar mai girma Gwamnan Jihar Kaduna na yi wa kowa adalci domin samun nasarar da ake bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here