Sun Kai Ta’aziyyar Rasuwar Abokin Karatunsu

0
177

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  Kalaba

KUNGIYAR  tsofaffin daliban makarantar sakandiren Karaye ta kai ziyarar ta’aziyya harin Rogo Karamar hukumar Rogo jihar Kano domin su yiwa iyalai da ‘yan uwan abokin karatun su da Allah ya yi wa rasuwa Alhaji Sani Usman Rogo .

Kungiyar karkashin jagorancin shugaban ta na kasa Dallatyn Karaye Alhaji Isah Ilya da makaranansa .

Kungiyar wadda akafi Sani da Karoba har wa yau ta ziyar gidan daya daga cikin abokin karatun nasu dake fama da matsananciyar jinya wato Alhaji Salisu Rogo,

Da yake yiwa wakilin mu na kudanci  karin haske game da ta’aziyar shugaban karoba na kasa Dallatun  Karaye ya ce kungiyar tsofaffin daliban ta na Kaiwa Duk Wani danta ziyarar sada zumunci tare da tallafawa idan yana cikin Wani matuwacin Hali “to a wannan karo mun dawo ne domin yiwa iyalai da ‘yan uwan Marigayi ta’aziyya idan baka manta ba kwanan Baya mun kawo wa Marigayi ziyarar duba shi lokacin yana raye Bashi da lafiya Sai gashi a wannan karo kuma Allah yayi Masa wa’adi mun kuma ziyarci daya abokin namu abokin karatu Salisu Rogo Wanda Shima jar yanzu yake fama da matsananciyar jinya.”Inji shi

Kungiyar tayi addu’a tare da roka Masa rahama da gafararr ubangiji .

Iyalan Marigayi Dana mara lafiyar sun bayyana ziyarar abar sada zumunci ce tare da yi musu Godiya da yi musu fatar Allah daka musu da alheri .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here