SIYASA TA JAWO YAN AREWA SUN RASA MAYANKAR FATAKWAL

0
224
MUSA MUHAMMAD KUTAMA , Daga Kalaba
YADDA  siyasa ta sanya ‘yan kasuwa da ke babbar mayankar Fatakwal  da ke Trans Amadu  unguwar masana’antu jihar Ribas ta sanya suka rasa mayankar a makon da ya gabata  gwamna Jihar Nsom Wike ya sanya aka rusa mayankar.
Bincike da wakilinmu na kudanci  ya  gudanar ya  gano cewa sama da shekara 30 kabilu Daban-daban da ke fadin kasar nan ne suke kasuwanci a kasuwar .
Dangantaka ta fata tsami tsakanin ‘yan kasuwar da gwamnan Jihar ne lokacin da zaben 2015 ya karato wani tsagi na yan kasuwar suka goya wa dan takarar gwamna karkashin jamiyyar APC yayin da kuma wani kaso ya yi dan takarar gwamna na jamiyyar PDP wanda shi ne gwamna mai ci yanzu Nyesom Wike.Bayan haka a tsakanin shugaban cin kungiyar mahauta ta kasa reshen jihar Ribas,an samun jani-in jaka  tsakanin bangaren Marigayi Alhaji maisundu Beli ,da shugaban kungiyar na yanzu Alhaji musa Baba bayan shafe Yan watanni ana tataburza tsakanin Yan Takara da wanda ake so ya sauka haka dai akayi yayi har Allah ya sa Alhaji Musa Baba ya zama shugaban kungiyar mahautan da kasuwar baki daya saboda irin karfi da tasirin rinjaye sana’ar yankan Dabbobi da ake yi ya sanya ‘yan Arewa ke shugabantar kasuwar .
Da zaben 2015 yazo Wike, ya nemi daukacin Yan kasuwar su goya masa baya sai aka yi raba-da -rabi Wasu suka Yi APC yayin da kuma sauran sukayi PDP wannan lamari ya sanya gwamma Nyesom da ba su zabe shi na ake zargin ya kullaci ‘yan kasuwar ya sanya shi rushe mayankar gaba da ya
Kazalika an rika dasawa da Nyesom Wike lokacin yana shugaban karamar hukumar Abiakppr da Yan kasuwar lokacin haka dai akaci gaba da zama gwamnan na neman sanadi kalilan ya rufe kasuwar kwatam sai ga cutar kurona ta bulla ya kulle kasuwar tsawon shekara daya da rabi kafin daga bisani ya rusa kasuwar .
Ko wane Hali Yan kasuwar suke ciki da kuma makomar su ? Wannan shi ne abin tambaya dangane da haka wata majiya ta shaida ma wakilin mu cewa “mutum bakwai ne suka yanke jiki suka fadi kasa rai yayi halin sa lokacin da aka zo rushe kasuwar”Inji majiyar
Wakilin mu yaji tabaki Alhaji Ali Danbaba  Zariya   mazaunin kasuwar wanda shi ma rusau din ya rutsa da shugunan sa ya ce”  Gaba daya kasuwar an rushe ta masallatai uku kadaii aka bar mana  ba’a mayar damu ko bamu Wani wurin na bilhasali ma ko maganar ma bai yi mana ba  ya zo ma ya yi mana wani kalami na kwantar da hankali ba.”
Yaci gaba da cewa “muna cikin halin lahaula Amma Yan uwan mu wasu sun tafi kwararo sun samu imda suka dan makale kuma tun lokacin lokacin kurona da ya kulle kasuwar shekarar mu daya da wata bakwai karshe wa’adin kwana 30 ya bamu yace mu tashi mu bar masa garin sa zai rushe kasuwar”
Alhaji Ali zariya yayi zargin ance gwamnan  saboda ” zaben 2015 wa’adina biyu bamu yishi ba Gaskiya bamu yishi ba ko lokacin ma da yake shugaban karamar hukumar Abiakppr ya karbi kudin mu naira milyan 60 shine da wata gwamnatin ta zo ta ce wannan kudi kada mu kara biya wannan abu ne ya dameshi  dama yayi ikarin cewa shi ba zai kore mu daga jihar sa ba Amma wahalar da zai ba mu ita ce zata koremu daga kasar sa mu ‘yan Arewa “.inji shi
Yanzu haka inji dan kasuwar Yan Arewa mazauna fatakwal dake babbar mayankar nata sulalewa suma barin garin sakamakon rushe musu wurin cin Sana’a”
Ya zuwa yanzu  tun daga lokacin da aka yi lakadawun (kulle kurona) sama da.mutum 40 me suka shiga mawuyacin hali wasu kuma sun hadiyi  zuciya suka mutu ko a lokacin da ya aiko zaizo a rushe kasuwar mu da masu rusau din suka zo a kalla mutum bakwai ne suka yanke jiki suka fadi  sanadin haka suka rasa rayukan su inji mazaunin kasuwar da aka rushe.”Dattawa kasuwar akwai kabilar Igbo,akwai Hausawa daga cikin su da suka hadiyi  zuciyar suka mutu”
Don kai Danjarida ne ya sanya zan gaya maka gaskiya.
Karshe ya shawarci Yan  Najeriya sa suyi hattara da gwamnan Ribas a kokarin neman shugabancin kasar nan da aka ce yana son yi bangaranci da kabilanci ne  a zuciyar sa kowa yayi hattara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here