NCMN Ta Ziyarci Gidan Marayu, Ta Bada Tallafin Kayan Abinci, Tufafi Da Sauran Abubuwa

0
394

DAGA; USMAN NASIDI KADUNA.

 

A BISA yunƙurin sanya murmushi da haɓaka ƙa’idar barin al’umma a cikin farin ciki tare da dabarun gwagwarmayar fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Kungiyar Kwamarodin Najeriya (NCMN), ta sha alwashin ganin cewa Marayu sun amfana daga ribar fafutukar gwagwarmayar da suke yi.

A yayin ziyarar bazata da suka kai gidan marayun yara na Al-Ihsan Baisuma, dake Nasarawa jihar Kaduna, a ranar Asabar, kungiyar ta bayar da tallafin kayan abinci, tufafi, da sauran abubuwa masu mahimmanci don tallafa wa marayun samun ingantacciyar rayuwa kamar yadda sauran Yara suke.

Shugaban (NCMN), Kwamared Jabir Ibrahim Yaro, ya yi bayanin cewa ziyartar gidan marayu da mutane masu ƙarancin gata, wani bangare ne na kudirinsu don tabbatar da cewa sun sanya farin ciki a cikin al’umma tare da ɗan abin da suke da shi kuma wanda ya yi dai-dai da tsarin gwagwarmayar Kungiyar ta su.

Ya ce, “Ziyartar gidajen marayu a kowace shekara a cikin watan Oktoba, yana cikin ayyukan Kungiyar kuma wannan ba shi ne karo na farko da muka zo wannan gidan ba don yin ɗan abin da za mu iya na tallafa wa yara don nuna ƙauna, yayin da mu kan yi wasa da su a matsayin wani ɓangare na mu. ”

NCMN Ta Ziyararci Gidan Marayu, Ta Bada Tallafin Kayan Abinci, Tufafi, Sauran Abubuwa

“(NCMN), ƙungiya ce mai zaman kanta wacce ba ta samun tallafi daga kowace ƙungiya ta gwamnati, baya ga membobin ta waɗanda ke da niyyar yi wa rayuwar ɗan adam hidima ta fannoni daban -daban, kuma koyaushe a shirye muke don ɗaukar gwagwarmayar neman ƴancin al’umma har abada don samun ingantacciyar al’umma. ”

Malam Jabir ya kara da cewa, kalubalen da mafi yawan marasa galihu ke fuskanta na zama wani abin firgitarwa, musamman a yankin Arewa kuma hakan na bukatar kowace al’umma su nuna kauna da kulawa ta yadda suka dace da nuna mahimmancin su, saboda akwai dayawa daga cikin mutane marasa gata a cikin al’ummar mu da suke da bukatar kulawa.

Shugaban (NCMN), ya roki al’umma da gwamnati a kan su mai da hankali sosai wajen inganta rayuwar mutane marasa galihu waɗanda yin hakan na iya samun taimakawa rage a ɗabi’ar rage laifuka a cikin al’umma, musamman yanzu da Arewacin ke fuskantar barazana.

NCMN Ta Ziyararci Gidan Marayu, Ta Bada Tallafin Kayan Abinci, Tufafi, Sauran Abubuwa

A yayin da take jinjinawa wannan karamci mai kyau, Shugaban dake Kula da Gidajen Yara na Al-Ihsan Baisuma, Malama Firdausi Yusuf Muhammad, ta nuna godiya ga irin wannan karamci da Kungiyar ta bayar na tallafawa gidan marayun don kyautata rayuwar marayun.

Ta kara da cewa, Gidajen marayu wurare ne da a koda yaushe suke fuskantar kalubale iri daban daban musamman na kayan abinci, kudin makaranta, tufafi da kula da lafiya wanda akoyaushe suke buƙatar kulawa, kuma yawancin mutane ba sa zuwa wurin su sai lokutan watan azumin Ramadana.

Shugabar Al-Ihsan Baisuma, Mai Kula da gidan marayun Malama Firdausi Yusuf Muhammad tare da wasu yaran

Ta ce, “ba lallai bane sai mutum ya dauki makuden kudade yazo ba don ko yaya tallafi yake muna godiya a kan shi, don mutum na iya sanya farin ciki a fuskokin Marayu ta hanyar zuwa kawai musu ziyara don yin wasa da yaran, ko fita da su, da taimaka musu ta wasu hanyoyi. kamar aski, yin kitso da sauran ayyukan da za su iya yin ranakun su. ”

Shugabar mai kula da gidan marayun Malama Firdausi, ta gode wa jagorancin (NCMN) kan ziyarar da take kai wa gidan marayu da Yaran, yayin da ta yi musu addu’ar samun nasara wajen cimma burinsu, ayayin fafutukar gwagwarmayar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here