Babu Wani Dan Takarar Da Ya Fi Atiku Cancantar Zama Shugaban Kasa – Kungiyar ANMA

0
120

Daga Wakilinmu.

WATA kungiyar matasa ta Atiku Ne Mafita A Najeriya dake fafutukar ganin dan takarar Jam’iyyar (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya zamo shugaban kasa a zabukan shekarar 2023, ta bayyana cewa babu wani sauran mafitar da ya ragewa kasar Najeriya face zabar Atiku Abubakar a matsayin wanda zai ceto Kasar daga cikin halin da ta ke ciki.

Shugaban kungiyar na Kudancin Kaduna, Mujaheed Muhammad ne ya bayyana haka bayan kammala taron kungiyar reshen karamar hukumar Jama’a a garin Kafanchan.

Ya kara da cewa a bisa la’akari da halin da kasar ta tsinci kanta a ciki tun bayan hawan gwamnatin APC da ya shafi tabarbarewar tsaro, tsadar rayuwa da rarrabuwar kan ‘yan kasa, babu wata mafita face zabar dan takarar da ya san kan tattalin arzikin kasar, wato Alhaji Atiku Abubakar.

Ya ce “bai kamata ‘yan Najeriya su sake rudewa da duk wani alkawarin bogi da Jam’iyyar APC za ta sake yi musu ba domin, duk abubuwan da su kayi mana alkawari a 2019 ne yanzu suke sake maimaitawa kuma suke kamfen da su wanda hakan ke nufin su da kansu sun tabbatar da cikin shekaru takwas ba su iya ceto kasar Najeriya daga duk irin matsalolin da suka ce tana damunta ba.”

“A yanzu, lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su gwada Atiku Abubakar domin shi ne wanda zai iya dawo mana da martabar Najeriya saboda kwarewarsa a fannoni daban-daban da kuma irin karbuwar da yake da shi a kowane sassa na kasar, ba wai a rika kokarin kakabawa mutane wani mutum na daban ba.”

“Lokaci ya yi da wasu tsiraru zasu daina firgita ‘yan Najeriya kan zabar Atiku don a yanzu shi kadai ne a cikin ‘yan takarar da kowace Jam’iyya ta tsayar wanda mabiya kowane addini daga dukkanin sassan Najeriya suka aminta da shi kuma yake martaba dokokin kasa dana hukumar zabe ba tare da bayar da ciwon kai ba.” Acewar Mujaheed

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here