Takarar Gwamnan Zamfara: Ana Fargabar Jam’iyyar PDP Na Iya Rasa Damar Ta A Zaben 2023

0
235

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

YAYIN da yakin neman zaben jam’iyyar PDP na takarar kujerar Gwamnan Jihar Zamfara ya koma dakin shari’a, masu ruwa da tsaki sun bayyana fargabarsu, inda suka ce kararraki da sauran wasu matsalolin da ba a warware ba na zaben fidda gwani na iya jefa jam’iyyar adawa a matsayi mafi girma na siyasa a Jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, kakakin wata kungiyar mai suna Concerned PDP Volunteers, Isa Kwatarkwashi ya koka kan yadda shugabannin jam’iyyar suka nuna rashin amincewarsu a Abuja wajen magance rikicin da ya dabaibaye zaben fidda gwanin Gwamna da aka kammala, ta hanyar yin adalci ga duk masu son tsayawa takara da suka yi zaben.

Kwatarkwashi, ya bayyana rikicin da ke faruwa a matsayin wanda zai iya cinye jam’iyyar da kuma lalata damar da ta samu na samar da Gwamnan Jihar Zamfara.

Ya kara da cewa rikicin cikin gida a jam’iyyar APC mai mulki a wancan lokaci ya janyo wa jam’iyyar takarar Gwamna a 2019, wanda hakan ya share fage ga wanda ke zaune a gidan gwamnatin jihar Zamfara, Bello Matawalle ya hau kujerar na daya a cikin Jihar.

Dan siyasar ya yi nunar da cewa, inda ba don tsohon Gwamnan Jihar AbdulAzeez Yari, Sanata Kabiru Marafa da sauran wasu shugabannin bangarorin suka haifar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar gujewa wani abu na kashin kai da fifita muradun jam’iyya fiye da wani abu, to da APC a lokacin ba za ta yi asarar jihar da tarin albarku ba ga Matawalle, Dan Takarar PDP a 2019.

“Dole ne mu guji maimaita mummunan tarihin da ya jawo faduwar wasu a fagen siyasar kasar nan.

“Dole ne mu koyi daga abubuwan da wasu suka samu kuma mu yi amfani da su don jagorar ayyukanmu ta hanyar tabbatar da cewa an yi abubuwan da suka dace.

“Rikicin cikin gida da ke haifar da cece-ku-ce a tsakanin shugabannin jam’iyyar da ke son ’yan takararsu shafaffu su rike mukamai, sukan kai ga halaka jam’iyyar a rumfunan zabe saboda fitar da ‘ya’yan jam’iyyar da ba su yarda da su ba, wadanda kawai dalilinsu na tsayawa zabe shi ne girman kai a maimakon hidima ga mutane da kasa.

“Wadannan rigingimun cikin gida sun yi ta faruwa a wasu jihohin da ya kamata mu dauki darasi daga gare su amma shugabanninmu sun shagaltu da yadda za su ciyar da son rai sama da ta jam’iyya.

“Wani kwatankwacin kuma shi ne abin da ke ci gaba da tabarbarewa a jihar Kaduna inda wani dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar PDP na shiyyar Kaduna ta tsakiya, Honarabul Usman Ibrahim wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya yi kuka da cewa an yi zabe na arangizon kuri’u fiye da kima ta hanyar wakilai, kuma Jam’iyyar ta bayyana Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mr LA a matsayin wanda ya lashe zaben kuma hakan yasa daukaka kara a gaban kotu yana neman a soke zaben.

“Sanatan Yobe ta Arewa wani lamari ne da ka iya kai karar kotu, inda masu iko a kodayaushe suke son bin tafarkinsu, hukumar zabe mai zaman kanta ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress na Yobe ta Arewa.

“Shugaban majalisar dattawan da ya yi ta kokarin karbar zaben Machina tare da hada baki da shugabannin jam’iyyar na kasa.

“Shugaban Adamu na kasa ya sanya Sanata Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan Yobe ta Arewa da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2023, yana mai cewa an gudanar da zaben fidda gwani a asirce inda ake zargin Lawan ya yi nasara.

“Wajibi ne a kira wannan mutumin da ke kan idon guguwar, Adamu Maina Waziri wanda ya tayar da rikicin, sannan a ajiye shi a inda yake – ma’ajiyar bayanai – idan har muna son mu ceci jam’iyyarmu mai daraja a Jihar Zamfara.

“Wannan zaben fidda gwani da Adamu Maina Waziri ya gudanar a karkashin jagorancin Col. Bala Mande ya bijirewa duk wani dalili na gaskiya, adalci, doka da ka’ida don haka ya kamata a duba idan har da gaske muke son mu dawo da gidan gwamnatin Zamfara a 2023,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here