Gwamna Buni Ya Ayyana Hutun Kwanaki 3 Ga Ma’aikatan Gwamnati Jihar Don Su Karbi Katin Zabe

0
140

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

GWAMNA Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya ayyana hutun kwanaki uku ga ma’aikatan Gwamnatin Jihar don su karbi katin zabe na dindindin (PVC) wato ranakun Laraba 29 zuwa Juma’a 1 ga watan Yulin 2022 kenan.

Bayanin haka na cikin wata sanarwa da mai rike da shugaban ma’aikatan Jihar, Alhaji Garba Bilal ya hannanta ga manema labarai a garin Damaturu, inda ya bayyana yin hakan zai baiwa ma’aikatan Jihar damar tafiya kananan hukumominsu domin yin rijista, gyara da karbar katin zabe na dindindin (PVC).

Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan ya faru ne saboda mahimmancin da gwamnatin Jihar ta dauka dangane da yin katin zaben ta yadda lamura ke gudana yanzu haka a fadin Kasar.

“Don haka gwamnan ya yi kira ga dukkanin illahirin ma’iakatan Jihar da su yi amfani da wannan dama don ganin wadanda basu da katin sun hanzarta don karbar sa ba tare da jinkiri ba.”

Wannan sanarwar ta kara da cewa an shawarci dukkan masu samar da sabis da masu gudanar da aikin da su kasance cikin shiri don ganin ba a samu wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here