Kotu Ta Amince Da Ci Gaba Da Sauraron Karar Shari’ar Sardaunan Badarawa Na Jam’iyyar PDP Kaduna

0
133

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA babban kotun Tarayya da ke zama a garin Kaduna, ta amince da ci gaba da sauraron karar Shari’a na Dan takarar Sanatan Shiyyar Kaduna ta tsakiya, a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Usman Ibrahim wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa, da mutum na farko wanda ya ke kara, wato Lawal Adamu wanda aka fi sani da Mista LA a bisa zaben fidda gwani na Jam’iyyar daya gudana.

A zaman shari’ar kotun da ya gudana a ranar talata wanda Sardaunan Badarawa ya shigar da karar abokin takararsa na zaben fidda gwani na Sanatan Shiyyar Kaduna ta tsakiya tare da wasu Ya’yan Jam’iyyar domin neman kadin a bi masa hakkinsa, Alkalin Kotun, Mai Shari’a Muhammad Garba Umar, ya bayyana amincewarsa na ci gaba da sauraron karar duk da rashin halartar wanda ake karar.

Rashin wanda ake kara na farko kuma wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na Sanatan Kaduna ta tsakiya na jam’iyyar PDP, Lawal Adamu da aka fi sani da Mista LA, a shari’ar, ya kawo cikas bisa ga ci gaban shari’ar da Alkalin ya yi barazanar ci gaba da shari’ar a zama na gaba.

Alkalin kotun ya ki amincewa da ci gaba da rashin halartar Mista LA ko kuma lauyansa a shari’ar duk da cewa an yi masa bayani ta hanyoyi daban-daban tare da sanarwar ranar bayyanar ta sammacin, ya kara da cewa idan har aka ci gaba da kaucewa halin wanda ake kara na farko ba za a bar shi da wani zabi don jagorantar shari’ar ba, face sai don ci gaba da sauraron karar.

Babban Lauyan Najeriya (SAN), Samuel Atung wanda ya gurfana a gaban kotun domin tsayawa Sardaunan Badarawa, tun da farko ya bayyana cewa ce an mika wa wanda ake kara na farko sammacin kotu, inda aka sanar da shi ranar da za a zauna zaman kotun domin gaggauta sauraron karar.

Atung ya yi mamakin dalilin da ya sa wanda ake kara na farko ya kasa bayyana duk da cewa ya san sauraren gaggawa da ake da kuma mahimmancin shari’ar, wanda a cewarsa shari’ar na da lokacin kammalawa.

Sai dai babban Lauyan shari’a bai ki amincewa da hukuncin da alkalin kotun ya yanke na baiwa wanda ake kara na farko wata damar uzuri ba ta hanyar dage shari’ar zuwa ranar Alhamis 30 ga watan Yuni domin sauraren karar.

Da yake jawabi ga manema labarai a harabar babban kotun tarayya Kaduna, wurin da aka fara shari’ar, Barista Atung ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda Mista LA ke ci gaba da kin zuwa wajen shari’ar wanda ya bayyana a matsayin almara.

“Kun ga yadda rashin wanda ake kara na farko ke kawo cikas a kan wannan muhimmin al’amari na shari’ar zabe da ke da kayyade lokaci.

“Kun ga yadda magoya bayansa ke yiwa wannan Kotu kawanya a duk lokacin da shari’a ta taso wanda hakan ke nuna yana sane da kwanan wata da takardun bayyanar da ya yi masa.

“Rashinsa na gaba a ranar Alhamis 30 ga watan Yuni ba zai hana Alkali ci gaba da sauraren karar ba saboda akwai lokacin da za a soke al’amuran zabe,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here