Wata Jami’a A Amurka Ta Karrama Shugaban Kungiyar AFAN Farouk Mudi

0
170

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

JAMI’AR Prowess dake kasar Amurka ta Karrama Shugaban Kungiyar manoma ta kasa, Dokta Farouk Rabiu Mudi da digirin girmamawa saboda gagarumar gudummawar da yake bayarwa ga ci gaban noma a Najeriya.

A wani kasaitaccen biki da aka yi a babban dakin taro na jami’ar Legas, an bayyana Dokta Farouk Mudi a matsayin shugaba wanda yake kokari sosai wajen kawo managarcin sauyi a fannin noma don wadata kasa da abinci kamar yadda manufofin wannan gwamnati suke.

Sannan an shaidawa mahalarta bikin cewa ” An baiwa Shugaban Kungiyar manoma ta kasa Farouk Rabiu Mudi digirin girmamawa na (Honoris CAUSA) saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa noma mai riba Bosa shugabancin sa, tare da jaddada cewa Kungiyar AFAN tana daga cikin kungiyoyi da ake alfahari dasu a kasar nan”.

An kuma karrama sauran mutane irin su sarkin noman Mambila, Alhaji Halidu da shugaban karamar hukumar Tsanyawa, Alhaji Kabiru Dumbulun da Uwar-gidan Gwamnan Jihar Bayelsa, Gloria Diri, sai Jakada Susan da shugaban hukumar kula da ma’aikata ta Jihar Ogun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here