An Bukaci Maniyyatan Hajin Bana Na Shiyyar Funtuwa, Dutsinma Da Su Hallara Sansanin Alhazai

0
116

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

BAYANAN da muke samu daga hukumar Alhazai ta Jihar Katsina na cewa hukumar ta kira ragowar Maniyyatan kananan hukumomin yankin Funtuwa da kuma wasu daga Dustinma da su hallara a sansanin Alhazai da ke kan hanyar Daura a Katsina domin shirye-shiryen tafiya kasa mai tsarki su sauke farali.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar jin dadin Alhazan Jihar Katsina Badaru Bello Karofi.

Sai kuma Maniyyatan shiyyar Dutsinma da kuma kananan hukumomin Batagarawa, Charanchi da Alhazan karamar hukumar Jibiya na shekarar 2020 kawai da su hallara a sansanin Alhazan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here