Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa Kamfanin ARMECO Bisa Gina Rijiyar Burtsatse Da Ta Kai Miliyan 10 A Wata Makaranta

0
134

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna ta yaba wa kamfanin “Arewa Metal Containers Limited” (ARMECO), bisa aikin gina rijiyar burtsatse da ta kai naira miliyan goma a daya daga cikin makarantun sakandaren gwamnati dake Jihar.

Da take jawabi a wajen bikin kaddamar da Rijiyar a makarantar sakandiren ’yan mata ta Gwamnati, (GGSS) Kakuri, Kaduna, kwamishiniyar ilimi, Halima Lawal ta ce, samar da ruwa a duk wani haraba na koyo yana inganta tsafta da lafiya.

Da ta ke wakilcin mataimakiyar a wajen taron, daraktan makarantun gwamnati, Misis Baita Mercy Kude, ta bayyana cewa kungiyar ta ARMECO ta taka rawar gani wajen yaba kokarin gwamnatoci wajen samar da ababen more rayuwa.

Halima, ta kara da yaba wa kamfanin bisa kara irin wannan karamcin musamman a muhallin makaranta ‘yan mata inda za su rika bukatar ruwa don kiyaye kansu da muhalli ma.

“Lokacin da yarinyar ke fama da al’ada na wata-wata kuma babu ruwan da za ta tsaftace kanta, ta kan ji rashin jin daɗi a cikin ɗakin karatunta, amma yanzu da ruwa ya samu, za ta yi abin da ake bukata kuma ta sami kwanciyar hankali tare da yin karatu cikin yanayi mai kyau.”

Kwamishinan, ta yi kira ga sauran kamfanoni da su yi koyi da ARMECO ta hanyar isar da irin wadannan abubuwan ga al’ummomin da suke karbar bakuncinsu.

Ta kuma yi kira ga hukumar makarantar da ta yi amfani da tsaftar ruwan sha ta hanyar kula da su akai-akai, ta kara da cewa, ruwa na ci gaba da rayuwa.

Manajan Daraktan ARMECO, Injiniya Joachim Daudu, ya ce rijiyar burtsatse na daga cikin ayyukan jin dadin jama’a da kamfanin ke gina wa al’umma da suke yin farin ciki da su.

A cewar injiniya Joachim, wanda ya samu wakilcin Manajan Kasuwanci, Alhaji Umar Bagudu, ba bayyana cewa ruwa wata bukata ce ta rayuwa wanda suke yin farin cikin samar da shi, yana mai cewa samar da shi zai yi tasiri ga rayuwar daliban.

Shugaban makarantar, GGSS Kakuri, Malam Abdussalam Adamu Abubakar, ya nuna godiya ga mai masaukin bakin inda ya ce, daliban sun sha fama da kalubale da dama kafin samar da rijiyoyin burtsatse saboda rashin ruwan sha.

“Ba a taba samun ruwa mai tsabta a makarantarmu ba, dalibanmu sun yi amfani da ruwan leda, amma da wannan gagarumin aikin, hatta yaduwar cutar za ta ragu, domin za a rika kiyaye abubuwan da suka dace sosai.” Inji shi.

“Mun samu wasu kungiyoyi irin su Peaugeot Automobile ta Najeriya, (PAN) da suka ba mu kayan daki, yanzu kuma ARMECO, muna godiya kuma muna addu’ar sauran kungiyoyi su yi koyi da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here