Tsohon Mataimakin Kwanturolar Hukumar Hana Fasa Kauri Ya Yi Allah-Wadai Da Rahoton Zargin Batanci Ga Buratai

0
155

 Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

TSOHON mataimakin Kwanturolan Hukumar hana fasa kauri (Kwastam) mai ritaya, Alhaji Ibrahim Isah, ya yi Allah-wadai da rahoton da wasu kafafen yada labarai suka yada na cewa an gano makudan kudade a gidan Laftanar Janar Tukur Buratai, Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin.

A kwanakin baya ne Wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta yi zargin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kwato naira biliyan 1.8 a gidan Buratai da ke Abuja.

Hakazalika ta yi zargin cewa wannan makudan kudaden na daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya ta ware domin siyan makamai da alburusai domin yakar ‘yan ta’adda.

Mukadddashin koturolan na kwostom mai ritaya, wanda shi ne Ciroma na Nguru, ya shaida wa manema labarai a Damaturu ranar Talata cewa, rahoton karya ne kuma dagangan aka yi don bata sunan Buratai, tsohon Shugaban Rundunar Sojin kasa (COAS).

Ya yi mamakin dalilin da ya sa wasu ‘yan jarida za su so su bata sunan Buratai, wanda ya yi wa kasa hidima na tsawon lokaci. 

“A Sani na, Buratai mutum ne mai rikon amana, dan kishin kasa wanda ba shi da aibu. Ba zan iya fahimtar dalilin da ya sa aka yi wannan shiri na tozarta shi ba haka siddan,” in ji Isah.

Ya kuma yabawa hukumar ICPC da ta wanke shi da cewa Buratai bai taba mallakar gidan da aka kwato kudin ba.

“Ta yaya irin wadannan makudan kudade za su kasance a gidan Buratai sama da shekara guda, bayan ya bar ofis ba tare da wani bincike ba, ko kuma tayar da hankali?

“Alal hakika, hukumar ta ICPC ta yi abin da ya dace a lokacin da ta yi gaggawar bayyana cewa Buratai ba shi da wata alaka da gidan da ake magana, wannan abu da ta yi abin alfahari cewar tana kwatanta gaskiya da adalci ayyukanta ba tare da bin son ran wasu ba. 

“Binciken da ICPC din ta yi a karshe ya nuna karara cewa gidan mallakin K. Salam ne, wani kamfanin gine-gine ne, wanda hakan ya baiwa masu zargin  kunya,” in ji Isah. 

Don haka ya yi kira ga hukumomin da ke kula da kafafen yada labarai da su sanya wa kafar yada labarai ta yanar gizon da ta aikata hakan takunkumin dangane wannan bata suna da ta yiwa jajirtaccen mutum irin Buratai. 

“Lokaci ya yi da masu kula da harkokin yada labarai za su tsaftace harkar yada labarai daga rashin gaskiya na wannan kafar sadarwa ta yanar gizo wadda ta kware wajen bata mutane baki daya.

“Aikin jarida, kamar yadda muka sani, sana’a ce mai daraja wacce take fadakarwa da wayar da kan al’umma kan gaskiya, ba labarai na karya da zage-zage ba.”

“Hukumomi na da alhakin gaggauta sanya wa wannan kafar yada labarai da sauran masu satar labaran karya takunkumi, domin dawo da amana da ‘yan Najeriya a kan kafafen yada labarai.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Isah ya kasance jami’in hukumar fasa kauri ‘Federal OPS Unit, Zone D, Bauchi, kafin ya yi ritaya a shekarar 2007. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here