ECOWAS Ta Buƙaci Jihar Gombe Da Ta Kafa Kamfanin Sarrafa Nama

0
166

Daga; Abubakar Rabilu, Gombe.

A KOKARIN ta na ganin ana samar da lafiyayye kuma ingantaccen Nama mai tsabta da bunkasa kiwon Shanu, gamayyar kungiyar kasashe masu arziki na yammacin Afirka (ECOWAS), ta hori Gwamnatin Jihar Gombe da ta samar da kamfanin sarrafa Nama.

Jagoran kungiyar ta ECOWAS PAC BAO 11 Project, Dokta Adetunji Jolaosho, ne ya yi wannan Kira a lokacin bikin kaddamar da bada horo na kwanaki hudu kan kula da Turkar shanu da kuma sayar da ingantaccen Nama.

Ya kara da cewa shirin wani hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Gombe da Kungiyar, inda bayyana cewa mafi yawancin Shanun da ake yankawa a Jihar ake sayarwa basu da koshin lafiya, wanda hakan ya sanya suka buƙaci a samar da kamfanin sarrafa Nama wanda zai taimaka wajen samar da tsabtatacce kuma lafiyayyen Nama ga al’ummar Jihar.

Dokta Adetunji, ya kuma ce banda batun lafiyar su, nauyin shanun da ake yankawa ma bai wuce kilogiram 200 ba, kana mafi yawan kasashen da suka ci gaba su kan yanka shanu ne da su kan kai kilogiram 600 zuwa sama.

Har ila yau ya Kara da cewa koda mayanka da ake da su wato (Kwata) basu da tsari suna bukatar a mayar da su irin na zamani.

A jawabin sa na kaddamar da bude taron, Kwamishinan ma’aikatar aikin Gona da gandun Daji, Muhammad Magaji wanda Daraktan Mulkin da kudi Suleiman Musa Kwami, ya wakilta, jinjinawa kungiyar ya yi bisa wannan shiri Inda yace ya ilimantar kwarai da gaske.

Daya daga cikin mahalarta taron Suleiman Sintali, ya ce yaji dadin wannan horo da aka basu kuma zai Kara sa shi ya inganta harkar turkar da yake yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here