Rikicin PDP Zamfara: Canjin Lauya Da Lawal Dare Ya Yi Ya Dakatar Da Ci Gaba Da Shari’ar Su

0
119

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

AN dakatar da sauraron shari’a kan karar da wasu ‘yan takara uku suka shigar a babbar kotun tarayya dake Gusau yayin da suke kalubalantar nasarar Dauda Lawal Dare bisa zaben fidda gwanin da ya gudana a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.

Masu karar su ukun su ne; Honarabul Ibrahim Shehu Gusau, Wadatau Madawaki da Aliyu Hafiz Muhammad.

Alkalin kotun, Mai shari’a Bappa Aliyu yayin da yake yanke hukunci kan karar da daya daga cikin wadanda ake kara, Dauda Lawal Dare ya shigar na neman a sauya lauyan, Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 29, 30 da 31 ga watan Yuli.

Lauyan Honarabul Ibrahim Shehu Gusau da sauransu, Barista Ibrahim Aliyu yayin da yake nuna rashin jin dadinsa kan matakin da wanda ake kara na 4 ya dauka na jinkirin shari’ar, ya ce saboda girman kai ne ya tilasta masa dage shari’ar.

Sai dai ya sake nanata kudurin wanda abokin shari’ar nasa ya yi na bibiyar shari’ar zuwa ga lamari mai ma’ana don saita abin da zai zama abin nuni a nan gaba, ya bayyana cewa hakan bai yi musu dadi ba.

“Mun kasance a gaban kotu a yau domin ci gaba da shari’ar da wadanda muke karewa suka shigar na kalubalantar sahihancin zaben fidda gwani na Gwamnan Jihar Zamfara na jam’iyyar PDP a ranar 25 ga watan Mayu bisa dalilan da suka gindaya na rashin bin ka’ida.

“Aikin ya ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokokin zabe wadanda idan aka bar su a ci gaba da zama ba zai haifar da ‘da mai ido ba a siyasarmu.

“Saboda haka, wani aikin kishin kasa ne a kanmu a matsayinmu na ‘yan kasa masu bin doka da oda masu kishin ci gaban dimokuradiyyar mu nemi gyara a gaban kotun kuma muna da kwarin gwiwar samun nasara a karshen wannan rana,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here