A Baiwa Kwankwaso Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

0
262

A MATSAYINA na dan Kasa kuma mai ikon yin magana kan al’amuran da suka shafi Kasar mu, ina mai amfani da wannan dama domin bada shawara ga mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyyar mu ta APC da dan takarar shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar APC da su baiwa tsohon Gwamnan Jihar kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso takarar Mataimakin Shugaban Kasa domin ci gaban kasar mu.

Duk da cewa muna da bambancin Jam’iyya, amma dai baiwa Kwankwaso takarar mataimakin Shugaban kasa zai haifar da alheri wajen bunkasa wannan kasa tamu mai albarka, musamman ganin cewa tsohon Gwamnan Jihar kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso yana da kyawawan manufofi ga wannan kasa tamu kuma shi ne ya dace ya kasance mataimakin shugaban Kasa a zaben 2023.

Bugu da kari, ina mai jaddada cewa Kwankwaso jagora ne mai kaifin basirar mulki da samar da ci gaban al’umma ba tare da nuna bambancin ra’ayi ko na kabila ba, wanda hakan ake bukata ga shugaba a tsari irin na dimokuradiyyar wannan zamani, tare da fatan cewa za a duba wanna shawara tawa domin samar da managarcin ci gaba a kasar nan.

A karshe, nan gaba kadan zan bayyana dalilai guda 7 da suka sanya nake bada shawara dangane da daukar Kwankwaso a matsayin mataimakin shugaban Kasa a zaben 2023 duk da cewa bama cikin jam’iyya daya dashi illa bukatar ci gaban kasa.

Alhaji Usman B. Dan Gwari, Unguwar Rijiyar Lemo, Karamar Hukumar Fagge, Jihar Kano.
(08034003230).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here