Hukumar NEDC Ta Kaddamar Da Cibiyoyin ICT A Jami’ar YSU Da FCET A Jihar Yobe

0
79

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

A WANI bangare na ayyukan ta na farfado da ayyukan sadarwa da rikicin ‘yan tada kayar baya ya kassara a baya , Hukumar Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC), ta kaddamar da sabbin cibiyoyi na ICT a Jami’ar Jihar Yobe, Damaturu da Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical), dake Potiskum.

Manajan Darakta na Hukumar NEDC, Mohammed Goni Alkali a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin, ya bayyana cewa Hukumar ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fasahar sadarwa domin samar da kwarin gwiwar matasa masu tasowa a yankin Arewa maso Gabas domin inganta ayyuka don zama  masu dogaro da kai.

Babban Manajan Daraktan, ya yi bayanin cewa hukumar (NEDC( ta samar da cibiyoyi 18 na ICT a fadin Jihohi 6 na Arewa maso Gabas da niyyar yaye dalibai kasa da 10,000 a duk shekara, wato kimanin dalibai 600 daga kowace cibiya.

Ya ce “Muna so mu tabbatar da cewa Matasanmu sun himmatu wajen samun kwarewa akan ayyukan sadarwa.”
 
Alkali, ya yi amfani da dandalin wajen sanar da cewa, hukumar ta (NEDC) ta kuma amince da gina dakin taro guda 250 a harabar jami’ar domin inganta koyo da sauran ayyukan ilimi.

Da yake magana kan wasu nasarorin da hukumar ta samu a fannin ilimi, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar (NEDC), ya kara da cewa hukumar ta fara aikin gina babbar makaranta guda daya a kowace shiyyar sanatoci uku na Jihar Yobe.

A nata bangaren, ministar harkokin jin kai da ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq wanda daraktan kula da ayyukan jin kai a ma’aikatar, Ali Grema ya wakilta, ta ce ayyukan za su taimaka wa kokarin Gwamnatin tarayya da na Jihohi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Da yake mayar da martani, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni wanda ya samu wakilcin kwamishinan ma’aikatar ilimi, kimiya da fasaha ta Jihar Yobe, Farfesa Muhammad Munkaila, ya yaba wa hukumar (NEDC) bisa wannan daukin da aka yi, inda ya ce jajircewar gwamnan Mai Mala Buni wajen bunkasa ilimi ya sanya ya ayyana dokar ta-baci a fannin na ilimi a Jihar Yobe.

Da yake gabatar da jawabin godiya, mataimakin shugaban Jami’ar Jihar Yobe dake Damaturu, Farfesa Mala Daura ya gode wa hukumar ta (NEDC) a madadin ma’aikata da daliban bisa wannan taimakon tare da bada tabbacin yin amfani da wannan wurin cikin adalci domin ci gaba da amfana. 

Ya ce “Jami’ar Jihar Yobe tana matukar godiya da taimakon ku da sauran alkawuran da kuka dauka.”

Tawagar ta zarce tare da duba wurin da aka gina dakin taron da zai dauki adadin mutane 250 da kuma gidaje 500 ga ‘yan gudun Hijirar a Jihar ICT Resource Center a FCET Potiskum da hybrid solar borehole a sansanin masu yiwa kasa hidima (NYSC) a Dazigau, karamar hukumar Nangere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here