Dokta Wailare Ya Godewa Al’ummar Dambatta Da Makoda Saboda Goyon Baya Da Su Ke Ba Shi

0
118

JABIRU A HASSAN,Daga Kano.

DAN takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya daga mazabar Dambatta da Makoda, Dokta Saleh Musa Wailare ya mika sakon godiya ta musamman ga daukacin al’ummar kananan hukumomin Dambatta da Makoda saboda kaunar da suke nuna masa.

Ya mika sakon ne a ganawar su da wakilin mu a daidai lokacin da ake shiga Sabuwar Shekarar musulunci, inda ya bayyana cewa tsakanin sa da mutanen mazabar tarayya ta Dambatta da Makoda, sai godiya da fatan Allah ya Kara dankon zumunci dake tsakanin su.

Dokta Wailare wanda shi ne Dan takarar wakilcin Dambatta da Makoda a majalisar wakilai ta kasa a tutar Jam’iyya PDP, ya nunar da cewa babu abin da zai ce da al’ummar wadannan kananan hukumomi biyu sai godiya tare da tabbatar da cewa in Allah ya tabbatar Masa da wannan kujera, ko shakka babu zai yi masu wakilci mai kyau da albarka cikin yardar Allah.

Dan takarar, ya yi alwashin cewa idan ya zamo wakilin Dambatta da Makoda a majalisar wakilai ta tarayya, zai yi kokari sosai wajen samar da ingantaccen ci gaba a mazabar tare da samar da ci gaban ilimi da hanyoyin dogaro dakai ga mata da matasa da kuma samo guraben aiki domin rage zaman saurare.

A karshe, Dokta Saleh Musa Wailare, ya mika sakon sa na fatan alheri ga al’ummar yankin da daukacin Musulmi duniya dangane da shigowa sabuwar shekarar musulunci ta 1444 bayan Hijira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here