Gwamnatin Jihar Borno Ta Rufe Wasu Manyan Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Guda 4

0
103

Dagda; TIJJANI USMAN BELLO, Maiduguri.

A BISA la’akari da dawowar zaman lafiya a wasu daga cikin Yankunan kananan Hukumomin da Yakin Boko Haram suka daidaita, kana aka raba su da muhallinsu sama da shekaru 10 da suka gabata, al’amrin da ya yi sanadiyyar sanya su zama ‘Yan Gudun Hijira a cikin garin Maiduguri bayan bude Sansanonin da Mahukuntan Jihar su kayi a wancan lokacin, Gwamnatin Jihar Borno ta rufe wasu sansanin da al’ummar suka koma garuruwan su.

abin da ya kaisu samun taimakon agajin gaggawa irin na Abinci, Ruwan sha, Muhalli, Asibitoci da dai sauran kayayyakin more rayuwa daga gwamnatoci da wasu Kungiyoyin da bana gwamnatiba.

Da yake jawabi yayin rufe sansanin yan gudun Hijiran Dalori 2 Camp, a ranar Alhamis din data gabata, Gwamnan Jihar Borno Furofesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa bisa la’akari da bukatar da ‘Yan gudun hijiran suka nuna na son komawa garuruwansu na asali don ci gaba da gudanar da rayuwarsu na yau da kullum ganin cewar an sami cikakken zaman lafiya a wadannan wuraren, to ya zama wajibi ne a bar kowa ya koma.

Ya kara da cewa Rundunar Soja ta (Opration Hadin Kai), ta tabbatar musu da cewa a yanzu kam Mutane za su iya komawa garuruwansu na asali don gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum kuma da wannan suke la’akari da cewa wajibi ne a matsayinmu na Shugabannin a’umma su goya masu bayan komawa garuruwannasu, tare da yin la’akari da taron nan na (Kamfala) da ya yi nuni da cewa komawan ‘yan gudun Hijira ya zuwa garuruwansu na asali ba za’a matsa mu su ba, domin za su koma ne don radin kansu.

Ya ce “dole ne a samar masu da ababen more rayuwa ta yadda za su gudanar da harkokin rayuwarsu cikin sauki da aminci kamar yadda muka rufe wadansu Sansanonin gudun hijra guda shida a baya, da wannan shi ne muke kafa hujja da mara masu baya, mu tanadar masu da duk abin da ya kamata su samu a garuruwannasu da zasu koma don gudanar da Sana’o’insu na Noma, Kiwo da Kasuwanci.

“Sannan muna aiki tare kafada da kafada da Asusun Tallafawa Wadanda suka Galabaita ta (VSF) a wannan Yakin na Boko Haram, domin tun da Gwamnati tarayya ta kafa wannan Asusu a karkashin Jagorancin Janar T.Y Danjuma, suke tare damu kuma suna kula da Mutanenmu ako wani irin hali suka shiga, suna bamu goyon baya tare da taimakon da ya dace.

“Wadannan Sansanonin yan gudun hijiran guda hudu, sun hada da Sansanin Gudun Hijira na Dalori 1, Dalori 2, sai Sansanin gudun hijira na kan Titin Gubio, dana na Muna garage, wanda kuma yawansu ya haura Dubu 10, wadanda suka fito daga Yankin Kananan Hukumomi biyar, da suka hada da Bama, Konduga, Mobar, Gubio, Gamboru Ngala, a yayin da kuma Yankin Karamar Hukumar Guzamala zasu kasance sai nan gaba, da haka nike kaddamar da wannan shiri na rufe wadannan Sansanonin yan gudun hijira guda hudu a yau dinnan.’’

Shi ko Kwamishinan Ma’aikatar Ginawa, Gyarawa da Sake Tsugunar da ‘Yan
gudun hijira a garuruwansu na asali ta (RRR), Injiniya Mustapha Gubio, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar ta kammala duk wasu shirye-shiryen da suka kamata wajen komawar wadannan ‘Yan gudun hijiran ya zuwa garuruwansu na asali, ta bangarori da dama, kama tun daga sake gina masu Gidajensu da ya lalace, da wasu Hukumomin gwamnati irin su Makarantu, Asibitoci, Ofisoshin ‘Yan Sanda, samar da Ruwansha, Gidajen Masarautu da dai sauransu.

Ya ce “da akwai wasu ‘Yan Gudun Hijiran da gwamnati ba ta san da suba, da kuma wadanda Gwamnatin ta san dasu, gaba daya kuma mun basu Kayayyakin Abinci, da kuma Kudaden da zasu iya
samun Jari su fara sana’o’insu na Noma, Kiwo da Kasuwanci ta yadda rayuwarsu zai iya komawa kamar yadda yake ada.

“Ko wani Magidanci an bashi Naira Dubu dari da Kayayyakin Abinci, tare da bayar da Naira Dubu 50, ga ko wace Mace, da nufin basu tallafin da zasu fara gudanar da rayuwarsu har ya zuwa lokacin da za su mike wa gaba daya.’’

Ita ma Babban Jami’a a Asusun Agazawa Wadanda suka Galabaita a Yakin Boko Haramu ta (VSF), Furofesa Nana Tanko, ta bayyana gamsuwarta da
irin tanade-tanaden da Gwamnatin Jihar ta yi na komawar ‘Yan gudun hijran ya zuwa garuruwansu na asali, in da ta kara da cewa suna aiki kafada da Kafada da Gwamnatin Jihar Borno, wajen ganin cewa an sami nasarar komawan wadannan ‘Yan gudun hijran ya zuwa garuruwansu na asali.

Ta ce “mun kuma tabbatar da cewa kowa da son ransa ya ke son ya koma sannan kuma an tanadar masu da duk wasu abin da ya kamata na abin da
ya danganci inganta rayuwarsu na yau da kullum, sai dai dan abin da ba za a rasa ba. Don haka, Asusunmu ya bayar da gagarumin gudunmuwa wajen komawarsu tare da kashe Makudan Miliyoyin Kudade har sama da Naira Biliyan 1.7, wajen wannan aiki ‘Yan gudun hijiran har sama da Dubu goma.”

Malama Falmata Bukar, tana daya daga cikin ‘Yan Gudun Hijiran da zasu koma garinsu na Banki a Yankin Karamar Hukumar Bama, kuma ta kwashe
shekaru 7 a wannan Sansani, inda ta bayyana cewa babu shakka tana farin cikin komawa garinsu na Banki, domin tana da yara bakwai, kuma tana tunanin irin yadda tarbiyarsu yake kasancewa a wannan gurun na Sansanin gudun hijiran.

Ta ce “basa samun zuwa Makaranta, sai Tallace-tallace da muke daura masu saboda suje su samo mana Abinci, ga matsalar samun Magunguna a Asibiti, da matsalar karancin Ruwan sha, da karancin Makewayi, sannan kuma mun dogara ne da Abincin da gwamnati da wasu Kungiyoyi ke kawo mana, to amma daga ranar da basu kawo ba, to shi kenan zamu kwana da Yunwa.”

“To amma kaga idan muka koma garin mu zamu samu zarafin gudanar da sana’o’inmu irin su Noma, Kasuwanci, da Kiwo, shi ya sa a yanzu muke nuna godiyanmu ga gwamnatin Jihar Borno wajen ganin ta tallafa mana mu koma garuruwan namu na asali.’’

Malam Bukar Ali, shi ma na daya daga cikin ‘Yan gudun hijran da zai koma garinsu na Konduga, wanda kuma ya kwashe shekaru 8 a wannan Sansani, ya bayyana cewa ya na cikin murna da farin ciki ganin cewa zasu koma garisu shi da Iyalisa bayan da rikicin Boko Haram y sanya su barin gidansu ba cikin shiri ba.

Ya ce “ina da Mata biyu da Yara 11. Mun rayune a cikin wannan Sansani cikin kunci da wahala, domin zaka iske mun wayi gari bamu da Abincin da zamuci idan har Gwamnati ko kuma wasu
Kungiyoyin da suke kawo mana ba su kawo ba, ga babu Makarantar da zamu sanya Yaranmu, ko shi kanshi wurin kwanan akwai matsala.

“To kaga kenan dole za muyi murna da komawarmu garuruwanmu na asali, domin zamu sami daman gudanar da Noma, Kiwo, Kasuwancu, Walda da Kere-kere, to kuma ka gani an taimaka mana da Abinci irin su Buhunan Shinkafa, Masara, Dawa, Taliya, Wake, tare kuma da Kudi har Naira Dubu
Dari don mu ja Jari, to wadannan ba shakka zasu taimaka mana a wajen gudanar da harkar rayuwarmu na yau da kullum.’’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here