Isa Ashiru Kudan Ya Taimakawa Yan Sa Kai Na Yankin Keke A Garin Kaduna

0
125

Daga; Mustapha Imrana, Kaduna.

DAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP, Honarabul Isa Ashiru Kudan ya yi kira ga daukacin al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da yin addu’o’in neman samun maganin matsalar tsaron da ke kara tabarbarewa a fadin Kasar Najeriya baki daya.

Isa Ashiru, ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci Unguwar Keke tun bayan da yan bindiga suka yi awon gaba da mutane sama da 30 a yan kwanakin nan.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Yakubu Lere, Daraktan yayata ayyukan Isa Ashiru da aka rabawa manema labarai.

Honarabul Isa Ashiru, ya ce Gwamnati mai ci a yanzu ta kasa aiwatar da aikin da ya rataye a wuyanta na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar Jama’a, madadin hakan ta bari komai ya koma a hannun yan bindiga masu Garkuwa da mutane suna neman kudin fansa saboda haka ya zama wajibi ga Jama’a da a ci gaba da yin addu’ar neman dauki daga Allah madaukakin Sarki.

Sanarwar ta kara da cewa dan takarar ya bayyana tausayinsa ga al’ummar da abin ya shafa, inda ya yi fatan Allah ya dawo da wadanda aka sace cikin Aminci.

Honarabul Isa Ashiru ya taimakawa da masu aikin sa kai da kudi naira dubu dari biyu (250,000) da suke aiki a yankin domin su samu damar sayen kayan aikin da suke bukata.

Tun da farko da yake gabatar da jawabin maraba, mai unguwa Alhaji Mutari Haruna, da ya barke da kuka, ya yi godiya da yabo ga Isa Ashiru da ya ziyarci su, kana ya bayyana cewa hakan shi ne na farko da wani shugaba da ya kawo masu dauki tun da yan bindiga ke zuwa unguwar tasu.

Alhaji Muntari ya kara da cewa ya na wannan kukan ne domin da akwai wasu mutanen da abin ya shafa amma ba wanda ya damu ya zo domin jaje ko taimaka masu har wasu kuma na ficewa daga yankin.

Ya ce “amma sai ga Isa Ashiru tare da tawagarsa ya zo domin jajanta mana, hakan ya nuna cewa shi mai tausayi ne da ya damu da jama’a.”

Al’ummar yankin dai sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin yi wa tawagar Isa Ashiru maraba, inda suka yi masa fatan alkairi da samun nasarar hidimar siyasar da aka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here