Sabuwar Shekarar Musulunci: Dokta Sabo Ya Yi Fatan Alheri Ga Al’ummar Bichi

0
109

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

DANGANE da shigowa sabuwar shekarar musulunci, Shugaban Karamar hukumar Bichi, Dokta Yusuf Muhammad Sabo ya yi fatan alheri ga al’ummar yankin da Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Kuma wakilin karamar hukumar a majalisar wakilai, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar da takwaransa na majalisar dokoki, Alhaji Lawan Shehu.

Sannan ya isar da sakon Sabuwar Shekarar ta musulunci ga majalisar dokoki da ta zartaswar Karamar hukumar tare da yin godiya dangane da goyon baya da hadin kai da al’ummar karamar hukumar suke bashi Wanda hakan ke haifar da samar da ci gaba ta kowane fanni na zamantakewar al’umma.

Haka Kuma Dokta Sabo, ya sanar da cewa da yardar Ubangiji majalisar Karamar hukumar Bichi za ta ci gaba da aiwatar da aiyuka na alheri ga al’umma ta yadda kowane bangare zai amfana da ribar dimokuradiyya ba tare da nuna gajiyawa ba.

A karshe, ya yi addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa tamu da duniyar musulmi baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here