Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa Ya Yi Fatan Alheri Ga Al’ummar Musulmi A Sabuwar Shekarar Musulunci

0
102

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

ZABABBEN Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa ya mika sakon sa na Sabuwar shekara ga al’ummar karamar hukumar da Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da maimartaba sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da kuma daukacin Musulmi baki daya.

Ya isar da sakon ne a ganawar su da wakilin mu, inda ya nunar da cewa akwai bukatar a kara yawaita addu’oi na musamman domin samun dawamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa ta mu Najeriya da kuma duniyar musulmi domin samun karuwar arziki cikin nasara.

Alhaji Ado Tambai ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da a ci gaba da yin aiki da koyarwar addinin musulunci musamman ganin yadda al’amura suke kasancewa a fadin duniya tare da fatan cewa Shekarar 1444 zata zamo abar alfahari da jin dadi a duniya inda Kuma yayi addu’ar samun gudanar da zabukan shekara ta 2023 cikin nasara.

A karshe, shugaba Ado Tambai Kwa, ya yi amfani da wannan dama wajen jaddada kokarin da majalisar Karamar hukumar Dawakin Tofa ke yi domin ganin rayuwar al’umma tana ci gaba da tafiya bisa albarka, tare da yin godiya ga daukacin al’ummar wannan yanki saboda goyon bayan da suke baiwa karamar hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here