Wani Dan Sanda Ya ‘Ɗirka Wa Ƴar Ƙanwarsa Ciki A Jihar Nasarawa

0
143

Daga; Rabo Haladu.

RUNDUNAR ‘yan sandan Najeriya ta damke wani jami’inta mai mukamin sufeto, kan zargin yi wa wata ‘yar kanwarsa, ‘yar shekara 15 fyade, da yi mata cikin shege a Jihar Nasarawa.

An kuma kama wasu mutum uku, ciki har da wani likita, dangane da wannan aika-aika.

Kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya, wato (FIDA), reshen Jihar Nasarawa ce wadda ta bankado labarin afkuwar wannan lamari, inda ta ce za ta ci gaba da bin diddiƙin batun, har sai ta tabbatar an hukumta duk wanda aka samu da laifi a al’amarin.

Bayanan da wakilinmu ya tattaro daga harabar hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, sun nuna cewa an damke jami’in ɗan sanda mai mukamin sufeto, wanda ke aiki a sashen tattara bayanan sirri a wannan runduna.

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra, wadda ita ce shugabar ƙungiyar (FIDA) reshen Nasarawa, ta bayyana cewa tun da farko sun samu rahoto ne daga wata cibiya ta tabbatar da adalci da zaman lafiya inda suka yi masu bayani kan wannan lamari.

“Da muka samu wannan labarin sai muka je B division a nan garin Lafiya inda muka je muka tarar da ƴan sanda, sa’annan aka kama insifekta ɗin da matarsa da ɗansa,” in ji Barista Rabi’atu.

“Sai muka kai yarinyar asibiti aka je aka yi gwaji aka tabbatar tana da ciki wata shida amma kuma an so a zubar da cikin, ɗan da ke cikinta ɗin ya mutu har kwana uku yana cikinta.

Ta bayyana cewa a rana ta uku ce suka kai ta asibiti inda har ta haifi ƴa mace wadda tuni ta mutu a ciki inda ta ce jaririyar har ta soma ruɓewa.

Barista Rabi’atu ta ci gaba da cewa yarinyar ta tabbatar cewa ɗan sandan ne ya yi mata ciki inda ta ce yakan dawo gida da lemu ko wani abin sha, amma ashe yana zuba mata wani magani ne a ciki, wanda duk lokacin da ta farka daga bacci sai ta ga jikinta duk ya ɓaci da jini.

A cewarta, sai daga baya yarinyar ta ankara ta gano cewa kawunta ne ke kwana da ita.

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra ta ce, kungiyarsu ta (FIDA) ta lashi takobin yin tsayuwar daka, wajen ganin an gurfanar da masu laifi a lamarin, a kuma hukunta su, domin hakan ya zama wani kakkausan gargadi ga wasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here