An Tabbatar Da Adalci Da Rikon Amana Na Hukumar NHRC A Jihar Borno

0
106

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri.

SAKATAREN dindindin na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu a jihar Borno, Alhaji Tahiru Shettima ya yi alkawarin baiwa ma’aikatar kula da hakkokin Bil-Adama ta kasa (NHRC) cikakken goyon bayan kan ayyukan da za su kai ga samun nasarar aiwatar da shirin adalci na gaskiya da rikon amana tare da tallafin Tarayyar Turai (EU) da Shirin Ci Gaban Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) a cikin 2021.

Babban Sakataren ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake ganawa da tawagar ayyuka na hukumar ta (NHRC) da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Maiduguri, domin ganawa da shi game da ayyukan da su ke yi na jin kai a wannan yanki na arewa maso gabas. 

Alhaji Shettima, ya ce falsafar ma’aikatarsa ​​ita ce bude kofa, hadin gwiwa, da jajircewa wajen ciyar da Jihar gaba. 

Ya ce “muna bude wa abokan hulɗar da ke son taimakawa wajen ceton halin da muke ciki, don haka za mu ba ku goyon baya dari bisa dari wajen aiwatar da Ayyukan ku”.

“Yancin dan Adam wani bangare ne na rayuwar dan Adam kuma babu wata al’umma da za ta ci gaba a inda ba a mutunta hakkin mutane. 

A cewarsa, a lokacin da ‘yan tada kayar bayan suka fara mika wuya, gwamnati ta fahimci cewa akwai bukatar yin amfani da hanya mafi kyawu don cimma burin da ake so na samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin, inda wadanda suka mika wuya da wadanda ke zaune a cikin al’umma za su samu matsaya guda, tare, domin ba dole ba ne a take hakkin dan Adam don cimma wannan.

“Me zai faru idan sun mika wuya?  Suna dawowa cikin al’ummominsu kuma yana da wahala a dabi’ance mutane su karbe su a cikin wadannan al’ummomin. Haka nan yana da matukar wahala a karfafa su zauna a cikin mutanen da suka yi wasu munanan halayya na take hakkin bil’adama.”

“Ba shakka aikinku zai ilimantar da jama’a tare da kwadaitar da su wajen rungumar zaman lafiya da sulhu musamman a lokacin da ake tafiyar da muhimman ayyuka na masu ruwa da tsaki kamar sarakunan Gargajiya, limamai da malamai, don haka za mu ba ku goyon baya fiye da kowane lokaci domin hakan ba kawai zai karfafa zaman lafiya ba ne, shi ya sa za mu ba ku goyon baya fiye da kowane lokaci, domin zai kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar Borno”. Ya ce

Tun da farko, mai ba da shawara na musamman ga babban sakataren gudanarwa wanda kuma mai kula da ayyukan, Mista Hilary Ogbonna, ya wakilta, ya bayyana cewa hukumar ta (NHRC) da abokan huldar ta na hada kai don aiwatar da wani shiri na inganta sulhuntawa, sake hadewa, da adalci a Jihohin Borno, Adamawa, da Yobe.  

Ya ce “daya daga cikin makasudin aikin shi ne tabbatar da cewa Jihohin da abin ya shafa sun daidaita yadda ya kamata tare da dawowar zaman lafiya  da yafewa juna laifukan da aka aikata.

Ya kara da cewa, akwai ayyuka da aka jera domin aiwatar da aikin kuma wani bangare na ayyukan shi ne taron sulhuntawa na gargajiya da na addini da aka shirya gudanarwa a tsakiyar watan Agustan 2022.

A cewar Mista Ogbonna, daya daga cikin manyan ginshikan shirin shi ne hadin gwiwa, don haka ne ya kamata a kai ziyarar ban girma ga masu ruwa da tsaki musamman wadanda ke cikin al’umma.

“Babu wani abin da za mu iya yi ba tare da cibiyoyin gargajiya ba. Muna so mu kira taron sarakunan gargajiya a Jihar Borno kuma muna neman hadin kan ku don ba mu damar gudanar da taron.” Mista Ogbonna ya ce.

Ya ci gaba da cewa, “da umarnin ma’aikatar ku muna kan inda ya dace don yin hadin gwiwa, mun dogara ne da ikon ku wajen isa ga mai martaba sarki da duk masu ruwa da tsaki a Jihar”.

Sauran mutanen da suka halarci taron sun hada da Daraktan kula da lafiya a matakin farko, daraktan harkokin masarautu, da sauran ma’aikatan gudanarwa na ma’aikatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here