Dan Kishin Kasa Ya Daura Tutar Najeriya A Kan Gidansa

0
101

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

WANI dan kishin kasa da ke zaune a cikin garin Kaduna Arewacin Tarayyar Najeriya ya bukaci al’ummar kasar da su rika sanya batun kishin kansu da kasarsu a gaba a koda yaushe domin komai ya kara inganta.

Mai kishin kasar ya ce saboda irin kishin da yake yi wa kasarsa ta haihuwa ya sa ya saura tutar Najeriya a kan gidansa da nufin kowa ya ga misalin yadda ake bayyana kishin kasa a wasu kasashen duniya da suka ci gaba.

“Na halarci wadansu kasashe a duniya kuma na ga irin yadda jama’ar kasar ke nuna kishin kasa ta hanyar daura tutar kasar a kan gidajensu wanda hakan na nuni da kishin kasarsu a fili, saboda haka ne muke kokarin nunawa jama’a domin kowa ya dauki sahun yin hakan”, inji dan kishin kasan.

Za a dai iya ganin hoton gidan da ke dauke da tutar Najeriya kamar yadda yake a hoton gidan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here