Shugaban Karamar Hukumar Bichi Ya Karbi Daruruwan Magoya Bayan Jam’iyyar NNPP

0
106

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

A RANAR Asabar din da ta gabata ne shugaban Karamar Hukumar Bichi, Dokta Yusuf Mohammed Sabo ya karbi daruruwan magoya bayan Jam’iyyar NNPP tsagin Kwankwasiyya zuwa Jam’iyyar APC a wani kasaitaccen taro da ya gudana a garin Santar Sabo.

Tun da farko a jawaban su daban-daban, wadanda suka sauya shekar, sun bayyana cewa sun gamsu da yadda Jam’iyyar APC ke gudanar da aiyukan alheri a yankunan su, sannan duk da halin tattalin arziki da ake fama dashi, karamar hukumar Bichi tana kokari sosai wajen samar da romon dimokuradiyya a fadin yankin ba tare da nuna gajiyawa ba.

Sannan sun sanar da cewa hakan ce ta sanya suka yanke shawarar canza sheka zuwa Jam’iyyar APC daga jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya tare da yin alwashin cewa zasu yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar ta APC ta sake lashe zabe a shekara ta 2023.

Masu canjin shekar sun yi amfani da wannan dama inda suka jinjinawa shugaban Karamar hukumar Bichi, Dokta Yusuf Mohammed Sabo da wakilin Karamar hukumar a majalisar wakilai ta tarayya, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar da wakilin Karamar hukumar a majalisar dokoki ta Jiha, Alhaji Lawan Shehu da dukkanin jagororin jam’iyyar saboda hada hannu da suka yi domin ciyar da yankin gaba.

A nasa jawabin, shugaban Karamar hukumar Bichi, Dokta Yusuf Mohammed Sabo ya bayyana cewa jam’iyyar APC tana da kyawawan manufofi don haka ita ce jam’iyyar da ta kamata yan Najeriya su rike tun daga sama har kasa, sannan ya jaddada cewa majalisar Karamar hukumar Bichi bisa jagorancin sa za ta ci gaba da aiwatar da aiyukan raya kasa ba tare da nuna kasala ba.

Wadanda suka canza shekar sun fito daga garuruwan Yalleman da Santar Inji da Yola da Sabo da Tar tasha daga mazabun Badume da Yanlami, sannan sun tabbatar da cewa shugaban Karamar hukumar Bichi, Dokta Yusuf Mohammed Sabo zai ci gaba da karbar mutane daga sauran jam’iyyu zuwa jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here