NUJ Kaduna Ta Taya Asma’u Yawo Murnar Samun Nasarar Zama Shugaban Kungiyar A Kotu

0
229

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

BIYO bayan hukuncin da wata kotun majistare da ke zamanta a Barnawa, karamar hukumar Kaduna ta Kudu a ranar Litinin din da ta gabata ta tabbatar da nasarar zaben shugaban Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, Kwamared Asma’u Yawo Halilu, cibiyar Kungiyar ta yi fatan alheri da yin maraba da hukuncin kotun tare da sadaukar da nasarar ga kungiyar da kuma daukacin mambobin Kungiyar.

Wata sanarwa da sakataren Kungiyar, Kwamared Gambo Santos Sanga ya sanya wa hannu, ta bayyana hukuncin kotun a matsayin wanda ke nuna hakikanin abin da akasarin ‘ya’yan kungiyar ke so, inda ta yi nuna cewa wannan al’amarin zai zama sanadin ci gaban Kungiyar ta NUJ a Jihar Kaduna.

Sanarwar ta kara da cewa, babu wanda ya ci nasara ko kuma akasin haka, yayin da ta kuma jaddada bukatar ‘yan jihar Kaduna ta kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya da su yi watsi da sabanin da ke tsakaninsu, su kuma yi kokarin ganin Kungiyar ta ci gaba.

Daga nan sai ta yi kira ga mambobin kungiyar ta NUJ da su manta da abin da ya faru a baya, su hada kai domin gudu tare kuma a tsira tare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here