Wani Kwamishinan Jihar Yobe Mai Ci Ya Rasa Ransa A Hatsarin Mota

0
86

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

KWAMISHINAN matasa da wasanni na Jihar Yobe, Honorabul Goni Lawan Bukar ya rasa ran sa sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da shi a jiya talata kan hanyar Damaturu zuwa Kano. 

Shi dai marigayi Goni Bukar, wanda aka fi sani da BUGOM, ya yi aiki a matsayin kwamishina a Gwamnatin Gwamna, Mai Mala Buni bayan da bai samu dacewar komawa ga majalisar wakilai ta kasa ba a 2019 sakamakon maye gurbin sa da aka yi da wani dan takarar. 

Wata majiya ta kusa da iyalin sa ta tabbatar da mutuwar Kwamishinan a wani sakon da aka wallafa a shafinsu na Facebook, da yammacin talata mai taken, “A huta lafiya, Goni Lawan Bukar, BUGOM”.

Kamin rasuwarsa jiya, Honarabul Goni Lawan Bukar, ya kasance kwamishinan ma’aikatar filaye, safiyo da ma’adanai, an zabe shi dan majalisar wakilai mai wakiltar Bursari/Geidam/ Yunusari kuma ya rike matsayi da dama a kwamitocin daban-daban a majalisar wakilai ta kasa.

Ubangiji Allah Ya jikansa da gafara, kuma Kyautata Karshen mu baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here