Ganduje Ya Samu Nasara A Mulkin Jihar Kano – Inji Kungiyar MDA

0
72

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AN bayyana cewa Gwamna, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sami dukkanin wata nasara da ake bukata a cikin mulkinsa duba da yadda Jihar Kano ta bunkasa daga shekara ta 2015 zuwa yau kuma ta kowane fanni.

Wannan bayani ya fito ne daga kungiyar Maigata Development Association (MDA) dake karamar hukumar Dawakin Tofa cikin wani sako da ta aikewa wakilin mu, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Dauda Mohammed Ali.

Kungiyar ta MDA, ta bayyana cewa cikin shekaru 7, Jihar Kano ta zamo abar misali cikin jihohin kasar musamman ta fuskar ci gaba da tattalin arziki da ilimi da kuma tsaro da zaman lafiya tare da bayyana Jihar kano a matsayin Jihar da ake zaune lafiya kuma cikin kwanciyar hankali”.

Haka kuma kungiyar ta sanar da cewa gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta yi kokari sosai wajen tsaftace siyasa da mutunta juna tsakanin manya da kananan yan siyasa, musamman a wannan lokaci na dimokuradiyya kamar dai yadda ake gani a halin yanzu.

A karshe, kungiyar MDA ta sanar da cewa nan gaba kadan zata fara wani shiri na wayar da kan al’ummar Jihar Kano bisa muhimmancin fita zabe domin ganin an gudanar da zabukan shekara ta 2023 cikin nasara, tare da yabawa gwamna Ganduje da daukacin mataimakan sa dake cikin gwamnatin saboda ci gaban da Jihar Kano ta samu tun da wannan gwamnatin ta karbi ragamar mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here