Za A Fara Amsar Katin Zabe A Watan Oktoba – Hukumar INEC

0
90

Daga; Hussaina Bala kanti, Kaduna.

SHUGABAN hukumar Zabe ta Kasa (INEC), reshen Jihar Kaduna, Dakta Asma’u Sani Maikudi, ta bayyana cewa za a fara amsar Katin Zabe da aka kammala yin aikin rajistan shi kwanan nan a watan Oktoba, na shekarar 2022.

Shugaban ta bayyana hakan ne a yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka gudanar na kwana daya a kaduna a ranar alhamis inda ta kuma cewa jam’iyyun siyasa 17 ne suke cikin takarar Gwamna a Jihar.

Dakta Maikudi ta kara da cewa a ranar 1 Augusta, 2022 akalla kiyasin mata kashi hamsin (50%) ne suka yi rigista katin zaben a fadin kasar.

A yayin da take jaddada karfin mata a zabukan 2023 , Shugaban ta bukaci mata da su marawa junan su baya tare da cewa goyon bayan juna shi ne mafi kyawun hanyar samun nasara a babban zaben 2023.

“Inaso inyi tawali’u da cewa masu tsara manufofin Najeriya kada su cigaba da mayar da mata saniyar ware a Najeriya domin babban illa ne ga kokarinta na ci gaba, a matsayin kasa mai dorewa.

“Duk wani tsari na dimokuradiyya da ya kasa hada ra’ayin jinsi aibi ne. Duk wani muhimmin tsarin dimokuradiyya dole ne ya haifar da ci gaban al’umma.” Dakta Maikudi ta bayyana haka.

Shugabar, a yayin da ta ke yaba wa gwamnatin Jihar kaduna ta ce : ” kaduna ita ce Jihar da ta zarce matakin da majalisar dinkin duniya ta dauka na kashi 35 a cikin 100 amma yanzun ta na kashi 47 na mata da aka dauka aiki a Jihar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here