Zaben 2023: Jam’iyyar APC Ta Sha Alwashin Samun Nasara A Yankin Arewa Maso Yamma

0
100

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SHUGABANCIN jam’iyyar APC mai mulki a yankin Arewa maso Yamma, ta bayyana cewa babu wata jam’iyya da za ta iya tsammanin samun nasarar lashe duk wani zaben a shekarar 2023 daga shiyyar baya ga Jam’iyyar ta APC.

Mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Yamma na kasa, Salihu Lukman ya bayar da wannan tabbacin yayin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna ranar Alhamis.

A cewarsa, sun jajirce wajen ganin jam’iyyarmu ta samu nasara a zabe mai zuwa, ta yadda babu wata jam’iyya da zata yi tsammanin za ta lashe zaben 2023 daga shiyyar Arewa maso Yamma saboda kawai suna ganin za su iya yin nasara.

Ya ce “Don tabbatar da cimma wannan buri, mun himmatu wajen samar da kyakkyawar alaka da shugabannin kowace jiha.”

Dangane da batun sulhu, mataimakin shugaban yankin arewa maso yamma ya bayyana cewa kwamitin da ke da alhakin gudanar da ayyukan, ta yi tasiri sosai kuma za su tunkari zaben a matsayin kungiya daya tak.

“Jam’iyyar ta yi farin cikin karbar mutane da dama da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyun siyasa zuwa namu, siyasa ita ce tattaunawa kuma kofofinmu a bude suke a kowane lokaci domin karbar sabbin mambobinsu,” Lukman ya jaddada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here