Akalla Kashi 70 Na Matasa Ne Su Ka Yi Rajistan Zabe A Shiyyar Arewa Maso Yamma – Inji Tsafe

0
104

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SAKATAREN tsare-tsare na jam’iyyar APC mai mulki a shiyyar Arewa maso Yamma, Salisu Uba Tsafe ya bayyana cewa matasa kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar Najeriya da suka yi rajista a aikin rajistar masu kada kuri’a da aka kammala.

Sakataren shirya taron na shiyyar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.

Ya bayyana cewa Shugabancin Jam’iyyar a shiyyar ba sa ja da baya musamman a fannin wayar da kan matasa da mata gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Sai dai Tsafe ya amince da hakan, duk da cewa lokacin yakin neman zabe bai yi ba, amma jam’iyyar na tsara dabarun yadda za ta hada kai da wayar da kan ‘yan Najeriya a fadin kasar domin kada kuri’ar APC a dukkan matakai.

A kokarinta na dorewar mulki a zabe mai zuwa, Tsafe ya bayyana cewa tuni jam’iyyar ta fara aiki da wasu kalubalen da ke fuskantar jam’iyyar, inda ya ce duk wani kalubalen da aka gano za a magance shi kafin a fara yakin neman zabe.

Dangane da batun shigar matasa a zabe mai zuwa, sakataren kungiyar na shiyyar ya ja hankalin matasa da su kasance masu kishin da tunani da kuma baiwa jam’iyyar dukkan goyon bayan da ake bukata.

“Muna kuma kira ga masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu musamman saboda yankin Arewa maso Yamma ne ya fi kowa yawan masu kada kuri’a wanda matasa ne suka fi yawa. Tsafe ya jaddada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here