An Yi Addu’o’i Musamman Domin Samun Zaman Lafiya A Katsina

0
103

Daga; Mustapha Imrana.

A RANAR Litinin din da ta gabata ne 1 ga watan Augusta shekara ta 2022, aka gudanar da addu’o’i na musamman a kananan hukumomin Funtuwa da Dandume da Bakori da Danja da karamar hukumar Sabuwa da ke Jihar katsina domin samun zaman lafiya da walwalar jama’a.

Dalilin wannan taron addu’o’in ya biyo bayan irin yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a yankin da yadda ‘yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka a yankin dama kuma sauran sassan jihar.

Addu’ar ta sami halartar manyan malaman izala da darika na dukkan kananan hukumomin yankin, kana addu’ar wadda ake kira da (yaumal shukur) wadda ake gabatarwa duk shekara, an gudanar da karatun Alkur’ani mai girma da sauran addu’o’i tunda misalin karfe 10 ma safiyar ranar da aka fara gudanarwa a dukkan dakunan taro na kananan hukumomin.

Dukkan shugabannin kananan hukumomin tare da hakimansu da kansilolin kananan hukumomin suka halarci taron Addu’o’in

A lokacin da suke nuna jindadinsu da kuma godiya ta musamman ga mai girma Gwamnan Jihar, Alhaji Aminu Bello Masari, Shugaban kananan hukumomin na Funtuwa, Malam Lawal Sani Matazu Wanda sakataren karamar hukumar Malam Salihu Danladi ya wakilta tare da hakimin Funtuwa Sarkin Maskan katsina, Alhaji Sambo idris Sambo da sauran manyan jami’an karamar hukumar da shugaban karamar hukumar Bakori, Alhaji Ali mai citta da hakimin Bakori, Alhaji Idris sule idris dana Danja, Alhaji Rabo Tambaya Danja da hakimin Danja, sarkin kudu Alhaji Bature da shugaban karamar hukumar Dandume, Alhaji Ya’u nowa da takwaran shi na karamar hukumar Sabuwa, Alhaji Faruku Hayatu da kogon katsina hakimin sabuwa, injiniya Bello Ibrahim sun yabawa dukkan malaman yankin da sauran jama’ar yankin ganin yadda suka tashi tsaye wajen gudanar da irin wadannan Addu’o’in domin samun zaman lafiya, kuma zasu cigaba da gudanar da irin wadannan addioin duk wata a dukkan kananan hukumomin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here