Editan Jaridar Africa Prime News Ya Rasa Mai Dakinsa

0
89

Daga; Habiba Abdullahi, Kaduna.

AN tabbatar da rasuwan Mai dakin edita, Mista Joseph edegbo na Jaridar Africa Prime News, wato misis Janet Iye Edegbo da suke zaune a kaduna da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Marigayiya janet ta rasu a ranar lahadi 31 ga watan yuli, 2022 bayan ta yi fama da wata gajeruwar rashin lafiya.

Ta rasu tana da shekaru 70 a duniya, kana ta rasu ta bar mijinta da ‘Ya’ya Tara, shida maza, uku Mata, kana da jikoki goma sha hudu.

Daga cikin ‘ya’yan ta, akwai mazayyani Bobby Enoch Edegbo, mazayyani Achile Edegbo, mazayyani Michael Ayegba Edegbo da kuma Injiniya Rogers Edegbo.

Sauran sun hada da, Mista Phillip Aduku Edegbo, Mista Emmanuel Edegbo, misis joy Achenyo Edegbo Amedu, misis Roseline Ejura Edegbo Haruna, da misis Josephine ojonugwa edegbo Abutu.

Hakazalika, an kammala shirye-shiryen yin bikin birne marigayyiyar.

A cewar iyalan mamaciyar, da akwai addu’ar tunawa da ita da za a gudanar a Cocin Christian Evengelical Fellowship Of Nigeria (CEFN), dake Kauri a Jihar Kaduna a ranar laraba.

Sannan, za a dauki Gawar daga garin Kadunra a ranar alhamis izuwa ga yan uwanta da ke garin Iyale a karamar hukumar Dekina a Jihar Kogi, na Arewa ta Tsakiya, baya ga haka za ayi Jana’izar ta a ranar Juma’a 12 ga watan Agusta a harabar Obaje bayan kammala addu’ar Coci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here