Kanikawa Sun Gudanar Da Gangamin Wayar Da Kan Matasa Kan Mahimmancin Sana’ar Hannu

0
142

Daga; Isah Ahmed, Jos.

DARURUWAN ‘Yan Hadadiyar kungiyar kanikawa ta Kasa (NATA), reshen Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sun gudanar da gangamin wayar da kan matasa kan mahimmancin kama Sana’ar Hannu.

‘Yan wannan kungiya wadda ta kun shi, masu sana’o’in gyaran mota da gyaran babura da walda da gyaran wayoyin wutar mota, sun gudanar da wannan gangami nasu ne, a bisa motoci da baburan hawa.

A wannan gangami ‘yan Kungiyar sun ziyarci manyan Sarakunan Saminaka da Lere da wasu hakimai da dagatan wannan yanki.

Har’ila ‘yan Kungiyar sun zagaya garuruwa Saminaka da Unguwar Bawa da Lere da Doka da Mariri da ke wannan yanki.

A zantawarsa da wakilinmu, Shugaban Kungiyar Kanikawan na Karamar Hukumar Lere, Alhaji Murtala Abdul’aziz ya bayyana cewa sun shirya gangami ne, don wayarwa da matasa kai, kan mahimmancin kama sana’a domin su dogara da kansu.

Ya ce idan mutum yana da sana’a ba zai sami damar yaje, ya aikata wani aikin ta’addanci ba.

Ya ce a wannan Kungiyar, wanda sun kai sama da mutum dubu, akwai wadanda suka kammala manyan makarantu.

“Babban burinmu shi ne mu bada gudunmawarmu wajen koyawa matasan wannan yanki sana’o’i, don ganin zaman lafiya ya cigaba da dorewa a wannan yanki”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here