Katin Zabe Ya Fi Bindiga Lahani – Aliyu Waziri

0
90

Daga; Mustapha Imrana.

AN bayyana katin zabe da cewa wani muhimmin makami ne da ya fi karfin bindiga lahani ga rayuwar al’umma musamman a wannan zamanin na Dimokaradiyya.

Honarabul Aliyu Muhammad Waziri, Santurakin Tudun Wada Kaduna kuma Dujuman Buwari da ake yi wa lakabi da Dan marayan Zaki ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da kafar yada bidiyo a kan dandalin Sada Zumunta ta Dimokuradiyya a ofishinsa da ke Kaduna.

Aliyu Waziri ya ci gaba da cewa shi a matsayinsa na dan Arewa da ake cewa Hausa Fulani, a batun wanda za a zaba nasa kawai ya sani, don haka duk mai jin maganar sa, to ba ta yadda zai dauki hannunsa ya zabi wani da ya fito daga Kudu, domin shi a matsayi sa nasa kawai ya sani”.

Sai dai Aliyu Muhammad Waziri Santurakin Tudun Wada Kaduna, ya bayyana wa duniya cewa shi da wani dan Mista Alban Ikoku da hotonsa ke jinin kudin Najeriya suka kirkiro harajin da ake kira VAT da Najeriya ke amfani da tsarin wajen samun kudin shiga, sai kuma shirin samar da tsaro na jami’an tsaron farin kaya na “Civil Defence” da a yanzu ake amfani da shi duk a wajen ciyar da kasa gaba.

“Akwai kuma tsare tsaren da suka hada da Noma da Kiwon Kajin turawa da ake horar da mata a yanzu da ake saran mata miliyan biyar za su amfana, sai kuma wani tsari tsakanin mu da wata kasa da za su kawo mana motocin Taraktocin Noma guda dubu 27 da har na dauko shugaban wancan kasar na kawo wa shugaba Buhari, Bayajiddan Daura”. Inji Aliyu Waziri Dan marayan Zaki.

Ya kuma tabbatar da cewa shi ya na nan cikin jam’iyyar PDP bai canza sheka ba, kuma zai ci gaba da yin amfani da iliminsa domin bayar da gudunmawarsa Najeriya ta bunkasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here