Wasu Kungiyoyin Manoma A Borno Sun Koka Bisa Rashin Samun Takin Zamani A Kan Lokaci

0
77

Daga; TIJJANI USMAN BELLO, Maiduguri.

A BISA la’akari da shigowar tsakiyar Damina, yayin da Manoma suka koma Gona don yin Shuka ko kumama Noman gaba daya a wasu wuraren, wasu
Kungiyoyin Manoman dake Kudancin Borno, sun koka saboda rashin samun Takin Zamanin a kan lokaci har ya zuwa wannan lokacin da Damina ya kankama.

Daya daga cikin mambobin Kungiyar, Malam Amos Ali, wanda ya fito daga Yankin Karamar Hukumar Hahul a Kudancin Borno, ya bayyana cewa duk da kasancewar sa Karamin Manomi, yana Noma sama da Hekta 10, yayin da yake Noma Shinkafa, Masara, Dawa da Alkama, to amma abin dake faruwa na rashin isowar Takin Zamani akan lokaci yana durkusar musu da wannan sana’ar.

Ya kara da cewa, a kowani shekara, suna samun irin wannan matsalar tun lokacin da wannan gwamnatin ta dare kan karagar mulkin wannan jiha, inda za a ga manoma sun shinrya tsaf da nufin cewa Damina ta fadi, za suyi ta Sharan Gona, su tanadi irin Shuka, to amma tsaikon jiran gwamnati ta kaddamar da shirin raba Taki ya hana su aiki, don kamar a bana ma har kawo wannan lokacin sun zuba ido amma har yanzu ba suga idon Takin ba.’

Ya ce, ’’Idan Damina ta yi nisa to sai kaga babu wani amfanin Takin, to kuma rashin Takin yana nakasar da Noma da kuma Manoman, a don haka muke kira ga gwamnatin jiha da ta yiwa Allah ta rika raba Takin Zamani ga Manoma a kan lokaci, don inganta aikin Noma a jihar dama Kasa baki daya.’’

Malam Abdu Isah, wanda ya fito daga Yankin Karamar Hukumar Biu, ya yi irin wannan korafin inda ya bayyana cewa shi ma yana Noma akalla Hekta 15, to amma rashin isowar Takin Zamani a kan lokaci yana dada durkusar da aikin na su, domin amfanin gonan na fara lalacewa tun yana Karami ganin cewar Kasarmu da su kansu irin Shukan sun saba da shi wannan Takin.

Ya ce “idan ba’a kawo da wuri an saka a shuka ba, sai kaga ana neman yin asaran Noman wannan shekarar, domin mukan tanadi Kudaden mu musanmman saboda wannan Takin, amma sai kaga bai zo ba, da a karshe mukan kashe Kudin ne ta wata hanyar ta daban, a don haka muna kira ga gwamnatin wannan jiha a karkashin jagorancin Farfesa Babagana Zulum, da ya yiwa Allah ya rika kawo mana wannan Taki da wuri.’’

Shi ko wani Manomin mai suna Yusuf Inuwa, cewa ya yi tun a farkon watan wannan shekarar da Gwamnan Jihar ta Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya Kaddamar da shirn baiwa Manoman Rani Kayayyakin Aikin Noman Rani ga Manoma sama da 500 Kyauta a Yankin Karamar Hukumar Monguno, babu wani abu makamancin wannan a Kudancin wanda ya hade Manya da Kananan Manoma da suke cin moriyar zaman lafiya tare da kasancewar yanayi mai Kyau a wannan Yankin nasu.

Ya roki gwamnatin wannan jiha da ta rika kai musu Takin Noman a kan lokacin domin komai tsadan da ya yi, za su iya saya, saboda yafi a ce ba a kawo musu ba.’

A nashi tsokacin, Mohammed Kolo, wani tsohon Manomi a Karamar Hukumar Damboa, ya bayyana cewa abin bakin ciki ne ainun ganin cewa wannan gwamnatin bata kawo musu Aro ko Hayan Taraktocin Noma kamar yadda take baiwa wasu bangarorin wannan jihar a lokutan Shuka ko kuma Girbi ba, balle kuma ayi maganar Takin Zamani.’

Ya ce “a yanzu haka, farashin Takin Zamanin ya yi tashin Gwauron Zabi idan Mutum ya kwatanta da farashinsa a Bara, inda a yanzu Buhun Taki na NPK da Urea masu nauyin Kg 50, ya kai Naira Dubu 20 zuwa Dubu 24, wanda farashin na Bara da ya kasance kasa da Naira Dubu 10, kuma a yanzu haka suke da wahalar samu ga Kananan Manoma musanmmama wadanda suka fito daga Yankunan Karkara.

Sai dai a wata takardar sanarwar da Mai baiwa Gwamnan Jihar Shawara a kan harkokin Yada Labarai, Tsare-tsare da Sadarwa, Malam Isah Umar Gusau, ya aikewa manema labarai ta Yanar Gizo-gizo a garin Maiduguri, ya yi nuni da cewa Gwmanan Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci wasu manoma a wasu Yankunan Kananan Hukumomi 4, dake fadin jihar, kana ya shaida masu cewa Koma bayan wadansu jihohin Najeriya, Gwmanatin Tarayya ta kakabawa Jihar Borno Takunkumin hana sayar da Takin Zamani saboda matsalar da jihar ta dade tana fama dashi irin na tsaro.

Sanarwar ta yi bayanin cewa tuni gwamnatin jihar Borno ta sami takardar Kakaba mata wannan takunkumi na hana mata sayar da Takin Zamani daga Ofishin Mai baiwa Shugaban Kasa Shawara a kan Harkar tsaro, saboda ana hasashen cewa ‘Yan Ta’adda suna yin amfani da daman na Takin a wajen sanya Manyan Muggan Makamai a cikin Buhunan Taki na NPK da Urea, da nufin a sayarwa da Manoma Taki amma Makamai ne a ciki, tare da yin amfani dashi wajen harhada Bama-bamai, wato (IEDs) a don haka suke karancin samun wannan Taki.’’

Gwamnan ya kara da cewa a saboda rashin Takin ne yake kara musu karfin gwiwar yin Noman tare da yin amfani da Taki irin na Gargajiya, da Magungunan Feshi gami da Ruwan Taki don bunkasa Noma Jihar, kuma Gwamnati za ta samar musu da nau’in Ruwan Taki a bana don bunkasa Noman.’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here