2023: Dan Barde Ne Ya Fi Dacewa Da Zama Gwamnan Gombe – Uwani Hamsal

1
230

Daga; Abubakar Rabilu, Gombe.

SHUGABAR kungiyar Reporters Awareness, kuma shugabar Mata ta tafiyan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, Muhammad Jibrin Dan Barde, Hajiya Uwani Hamsal, ta bayyana cewa Dan Barde ne yafi dacewa da zama gwtamnan Jihar Gombe a zaben shekarar 2023.

Hajiya Uwani Hamsal, ta bayyana hakan ne a lokacin wani taron manema labarai da ta kira a Gombe inda ta ce lokaci ya yi da al’ummar Gombe za su yi karatun ta natsu wajen gane wanda yafi kamata da mulkin Jihar a zabe mai zuwa.

Ta ce “gwamnatin APC ta gaza domin har yanzu da zabe ya yi kusa gwamnatin kara bakin jini take yi domin har yanzu magoya bayan jam’iyyar ficewa suke yi suna komawa PDP saboda adalcin jam’iyya.”

A cewar ta, Muhammad Jibrin Dan Barde, yana da Ajandoji uku zuwa hudu da zai fi mayar da hankali a kan su muddin aka zabe shi.

Ta ce “Dan Barde zai inganta bangaren Ilimi, da aikin Gona da tallafawa Mata da Matasa sannan kuma zai kawo abubuwan ci gaba da kowa zai amfana.”

Hajiya Uwani, ta kara da cewa har yanzu harkar ilimi tana sahun baya idan yazo zai daga ta saboda Ilimi shi ne tushen rayuwa.

A bangaren Noma kuwa tace nasu tsarin Dan Barde ya sha alwashin cewa shi ba zai kaddamar da Taki kuma azo babu Takin ba, shi idan ya kaddamar da Taki ya zama dole Manoma su samu kuma a farashi mai rangwame.

Uwani, ta kuma ci gaba da cewa Dan Barde, yace Mata za su samu kashi 35 cikin 100 da suke nema na mukaman gwamnati idan ya zama gwamna.

Sannan a cewar ta Matasa kuma da yake da su ake shan wahala, za su samu ayyukan yi dan dogaro da kan su sannan kamar yadda baya saba alkawari haka bai son mai saba alkawari idan ya fadi cewa zai yi abu yana cikawa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here