HAJJIN 2023: NAHCON Za Ta Fara Shirin Aikin Badi Domin Gujewa Samun Matsala – Hukuma

0
240

Daga; Abdulmalik Jibril, kaduna.

HUKUMAR Alhazai ta Najeriya (NAHCON), ta bayyana shirinta na fara shirye-shirye tun da wuri domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 mai zuwa da gujewa faruwar duk wata matsala.

Hukumar wadda ta nuna rashin jin dadin ta kan abubuwan da ba a zata ba kamar matsalar IBAN da ta shafi wasu Ma’aikatan yawon bude ido a aikin hajjin da aka kammala kwanan nan, ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a fara tantance kamfanonin jiragen sama.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’ar hulda da jama’a na NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar, inda ta kuma bayyana cewa hukumar za ta tabbatar da cewa duk wata yarjejeniya ta kwangila da aka rattabawa hannu ta cika kamar yadda aka amince da ita don taimakawa aikin hajjin mai zuwa.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar ga manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, ta bayyana cewa jirgin na karshe na zuwa ne kwanaki shida gabanin wa’adin jigilar mahajjatan kamar yadda hukumomin Saudiyya suka kayyade.

Sanarwar ta bayyana cewa: “Jigi na karshe na Najeriya na Hajjin 2022; Jirgin Azman Air dake dauke da mahajjata 319 daga Kaduna da Kano da jami’ai daga Jihohi daban-daban da NAHCON, ya tashi a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz Jiddah, a yau 7 ga Agusta 2023 da misalin karfe 12:00 na dare.”

Hukumar ta amince da cewa an samu kalubale yayin balaguron fita daga Najeriya zuwa Saudiyya, sakamakon karancin lokaci da sauran manyan kalubale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here