Adamu Mai Gemu Ya Yaba Wa Sanata Barau Jibrin Kan Samar Da Asibiti A Garin Kwa

1
180

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

WANI tsohon hedimasta kuma dan siyasa mai yin sharhi kan al’amuran yau da kullum dake garin Kwa, Alhaji Adamu Hedimasta Mai gemu ya mika sakon sa na godiya ga sanatan Kano ta Arewa, Sanata Barau I. Jibrin Saboda Samar da asibiti da ya yi a garin Kwa cikin aiyukan sa na mazabu domin kula da lafiyar al’ummar wannan yanki.

Ya yi wannan godiya ne a ganawar su da wakilin mu a garin kwa, inda kuma ya bayyana cewa samar da wannan asibiti zai taimaka sosai wajen rage doguwar tafiya neman magani a wasu asibitoci, sannan za a rika gudanar da wasu shirye-shirye na kula da lafiya cikin sauki musamman ganin yadda yankin yake da dumbin al’umma.

Alhaji Adamu Hedimasta mai Gemu, ya kuma yi kira ga sanata Barau Jibrin da ya taimaka a kai likitoci asibitin domin fara aikin kula da lafiya wanda hakan zai sanya a amfani kokarin da ya yi wajen samar da wannan asibiti mai albarka, tare da godewa dukkanin wadanda suke da hannu wajen samar da asibitin.

A karshe, mai Gemu ya jaddada cewa da ikon Allah al’ummar wannan yanki zasu ci gaba da yin amfani da asibitin kamar yadda ake bukata domin moriyar su da kuma ‘ya’ya da jikoki masu tasowa nan gaba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here